✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rediyon Jihar Katsina ya lashe kofin Gwamna Masari

Kungiyar kwallon kafa ta gidan rediyon Jihar Katsina ta yi nasarar lashe kofin Mai girma Gwamnan Jihar Alhaji Aminu Bello Masari a gasar wasannin da…

Kungiyar kwallon kafa ta gidan rediyon Jihar Katsina ta yi nasarar lashe kofin Mai girma Gwamnan Jihar Alhaji Aminu Bello Masari a gasar wasannin da kungiyar ‘yan jaridu marubuta labarin wasannni ta jihar ta shirya a tsakanin kafofin yada labarai da ke cikin jihar ta Katsina. 

An gudanar da wasan karshe ne  a ranar Alhamis ta makon jiya a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke cikin garin na Katsina.

An buga wasan ne a tsakanin ‘yan wasan gidan rediyon jihar da kuma na gidan talbijin wanda shi ma mallakar gwamnatin jahar ne a inda gidan rediyon ya saka kwallon da ake wa lakabi da “ci daya mai ban haushi”, ta hannun dan wasanta mai suna Shafi’u Aminu. 

Kamar yadda Manajan gidan rediyon Alhaji Sani Bala Kabomo ya ce a yayin da yake karbar kofin daga hannun danmadamin Katsina Hakimin Daddara Alhaji Usman Usman a madadin kungiyar, “tun farkon fara wasan zuciyata ta ba ni cewa ‘yan wasanmu ne za su dauki wannan kofi ganin irin yadda na ga bajintarsu. Kuma tun da aka fara wannan gasa sau daya aka saka kwallo a ragarmu inda muka ci 2 aka ci mu daya a wasan da muka yi da ma’aikatar yada labarai da harkokin cikin gida ta jihar”. Kamar yadda Manajan gidan rediyon ya ce,samun wannan nasara ta kara masa kwarin gwiwa a kan shirinsa na bullo da harkokin wasanni a harabar gidan rediyon domin bai wa ma’aikata da ma masu sha’awar wasannin motsa jiki damar zuwa don motsa jikinsu. 

Ya kara da cewa, tuni ake gudanar da wasan kwallon tebur a cikin harabar gidan. Sannan ya ce, sanin kowane cewa har shiri ke akwai na labarin wasanni a cikin shirye-shiryen da gidan rediyon ke gabatarwa. 

Alhaji Sani Kabomo ya jinjina wa gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Masari a kan irin yadda take bai wa bukatun kowane sashe na al’ummar jahar damar cinma burinsu wanda hakan ne har ya jaza Gwamna bayar da wannan kofi domin a yi wasan kara sada zumunci a tskanin kafafen sadarwa da ke aiki a cikin jahar.

Ita dai kungiyar ‘yan jaridun masu rubuta labarin wasanni SWAN ta bullo da wannan tsari ne domin kara farfado da harkokin kungiyar a jiha tare kuma da kara sada zumunci da fahimtar juna tsakanin kafafen yada labaran da ke cikin jihar. Ba wasan kwallon kafa kadai kungiyar ta shirya yin gasa a kansa ba, sai dai shi ne ya fi fice saboda irin tasirin da wasan yake da shi a duniya baki daya.

 Kafofin yada labaran da suka shiga cikin wannan gasa sun hada da Ma’aikatar Yada labarai na ma’aikatar harkokin cikin gida da raya al’adu da gidan talbijin na kasa da na jiha, wato NTA da KTTb, sai tashar Fm ta rediyon tarayya da kuma bision Fm mai zaman kansa sai shi gidan rediyon jahar wanda ya yi nasara.