✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rayuwar mata a Arewa na cike da kalubale- Rahama Sadau

Fitacciyar jaruma, Rahama Sadau ta ce rayuwa mata da suke da burin zama wani abu a yankin Arewa na cike da kalubale. Rahama ta bayyana…

Fitacciyar jaruma, Rahama Sadau ta ce rayuwa mata da suke da burin zama wani abu a yankin Arewa na cike da kalubale.

Rahama ta bayyana hakan ne a wani zantawa da ta yi da Jaridar Thisday.

Idan ba a manta ba, qungiyar MOPPAN ta dakatar da Rahama bisa zarginta da nuna dabi’ar da bata ba a cikin wannan faifan bidiyon da ta fito na wani mawaki mai suna ClassiQ dan garin Jos.

 Sai dai Rahama ta ce dakatar da ita da MOPPAN ta yi, ya zama mata sanadiyar samun daukaka a nan gida Najeriya, da wasu qasashen duniya.

Hakanan kuma ‘yar fim din ta ce za ta ci gaba da  kokari wajen kula da al’adarta da kuma tarbiyyarta a duk lokacin da  za ta shiga wani fim na bangaren Kudu.

A wani rahoto kuma, an ruwaito cewa Rahama Sadau ta ki amincewa ta fito a matsayin ‘yar madigo a wani fim saboda yadda fim din ya saba wa al’adarta.