✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rayuwar Dabbobi: Tattabara uwar alkawari

Tattabara na daya daga cikin tsuntsaye ko dabbonin da jama’a ke sha’war kiwo a gidaje. Bayan haduwar tantabara a matsayin mata da miji, tare za…

Tattabara na daya daga cikin tsuntsaye ko dabbonin da jama’a ke sha’war kiwo a gidaje.

Bayan haduwar tantabara a matsayin mata da miji, tare za su ci gaba da rayuwa suna kwai suna kyankyashewa a lokuta daban-daban.

Tattabara na iya tsara shekarsu a wurin da aka tanada musu, kamar daki, ko akulki da sauransu.

Sabanin sauran tsuntsaye da suke barin sheka su sake wuri bayan kyankyashe kwansu, su kuwa tantabaru ci gaba da amfani da shekar suke yi suna saka kwansu suna kyankyashewa, suna yayewa har sai abin da Allah Ya yi.

Kwan tattabara
Kwan tattabara

Tattabaru kan yi amfani da bawon kwan da suka kyankyashe da fukafukan da suka ciccire wajen tsara shekarsu.

Bayan tsara shekar kafin saka kwai, sai macen tantabar ta kwanta a shekar na wasu ‘yan kwanaki.

Galibi kwai biyu-biyu suka fi sakawa. Idan ta saka kwan farko, sai bayan sa’o’i 44 sannan ta saka na biyun.

Bayan saka kwai, miji da matar tare za su yi kwanci har na tsawon kusan kwana 18 ko fiye da haka kafin su kyankyashe.

Duk da dai tare suke kwancin ta hanyar karba-karba, amma macen ta fi yin kwancinta da yamma da daddare da kuma safe.

Yayin da daya ke kwance kan kwan, gudan kuma zai yi amfani da wannan lokaci wajen neman abinci.

A ranar kyankyasa, matar ce za ta kasance a kan kwan dodar, babu barci, babu zuwa kiwo.

Sabanin galibin tsuntsaye wanda suke shafe makonni biyu wajen renon ‘ya’yansu a sheka, yakan dauki tantabara kusan makonni hudu ko fiye da haka wajen renon ‘ya’yansu a sheka.

Sabon kyankyasa
Sabon kyankyasa

Uwar da uban, tare sukan yi aikin ciyar da ‘ya’yan har su zama ‘yan shila lokacin da za su iya fira da zuwa kiwo da kansu.

‘Yan shila na zama masu dogaro da kansu ne bayan makonni hudu zuwa shida da kyankyasa.

Galibi yadda aka kyankyashe ‘ya’yan tattabara haka za su tashi tare su zama mata da miji (aure) su hayayyafa.

Yakan dauki kimanin wata bakwai kafin ‘ya’yan su kai munzilin balaga, saduwa da juna da kuma fara saka kwai.

Tattabara na da zafin nama da fira zuwa nesa, wannan ya sa akan yi amfani da su a matsayin ‘yan aike wajen isar da sakonni da wasan tsere a wasu sassan duniya, bayan an ba su horo na musamman.

Duk da dai wasu na ra’ayin tantabaru na iya yada cuta a cikin al’umma, wasu masana na ganin wannan batu ba shi da karfi saboda a cewarsu, tantabaru tsuntsaye ne masu tsabta wanda hatsarin su yada cututtuka takaitacce ne.

Tattabara dauke da sakon wasika
Tattabara dauke da sakon wasika

Ana samun tattabara masu launi daban-daban, kamar fari, baki, fatsi-fatsi da sauransu.

Tattabara uwar alkawari in ji masu azancin magana, wai komai dare gida za ta kwana.