✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rayuwar aure: Matar Bahaushe sarauniya ce

A lokacin da Musulunci ya zo kasar Hausa ya riski wasu kyawawan al’adun Hausawa masu kama da na musulunci, kamar aure da zumunci da sutura…

A lokacin da Musulunci ya zo kasar Hausa ya riski wasu kyawawan al’adun Hausawa masu kama da na musulunci, kamar aure da zumunci da sutura da sarauta da sana’oi da kasuwanci da sauransu.
Auratayya ce jigon yaduwar al’umma, wannan ta sanya kabilu da yawa suke gogoriyo wajen kulla aure domin samun yalwa da yaukaka zumunci. Musulunci ya umarci duk wani baligi ya yi aure in yana da wadata. Hausawa sun jima suna auratayya tun kafin zuwan musulunci, amma a yau an wayi gari ana cewa sun fi kowace kabila yi wa aure rikon sakainar kashi, shin me ya faru? Talauci ko jahilci?
Sam ban yarda da wannan kazafin da aka yi wa Bahaushe ba! Shin ‘yan uwa kun leka kun ga yadda sauran kabilun suke zamantakewar aure, a fadar wasu wai Bahaushe ya mayar da aure tamkar riga, ni kuma na ce a’a, dole ka jinjina wa Hausa-Fulani wajen juriya a kan rikon aure, sabanin sauran kabilu wanda lalaci da mutuwar zuciya ya dabaibaye zamantakewar aurensu. Aure ne da suka shirya shi cikin rashin tausayi ta hanyar kashe dukiya mai tarin yawa, wannan ne fa ya sanya galibi ba sa aure da wuri har sai sun manyanta.
A zamantakewar aurensu, daga masu kudinsu izuwa talakansu to dole a raba hidimar gida, kama daga abinci zuwa makarantar ’ya’yansu. Aure ne da aka kulla na mutu kara ba, komai wulakanci. Mata ko da mazinaciya ce to dole miji ya zauna da ita, kuma matansu sun fi shan wahala, domin za ka iske kulllum suna tallace-tallace a titi ko aikin leburanci, kamar daukar kankare ko dako a kasuwa, ka je kasuwanni Legas nan za ka tausaya wa matansu. Mazajensu kuwa suna gidan giya ko caca babu ruwansu da hidimar gida domin aurensu mutu kara ba ne, kuma har abin hawa da dinki suke yi wa mazajensu, ‘ya’yansu kwata-kwata ba sa tausayin iyayansu, domin ba su isa su amfana daga dukiyarsu ba, anya duk lalacewar Bahaushe haka za ta iya kasancewa gare shi? Tabbas komai lalacewar Bahaushe da yadda ake zarginsa yana wulakanta aure to ba na ji zai iya barin matarsa ta fita titi, tana talla ko leburanci ko dako a kasuwa, ko kuma ya bari karti su rika shiga gidansa wai a matsayin ‘yan uwan matarsa. Amma saboda rashin adalici irin wannan zamantakewar auren mai kama da bauta sai a ce tsarinta ya fi na Bahaushe, duk da cewa saki a wurin Hausawa abu ne mai sauki, amma yinsa ya fi a zauna cikin kunci da bacin rai, domin a Musulunci cikin Suratul Al-ahzab Allah Mai girma da daukaka Ya ce bai halatta mumuni da mumuna su kasance cikin kunci, Allah Shi Ya ambaci saki, amma in an yi shi kusan sama da kasa kamar za su hade, idan kun yi dubi a kan sauran kabilun da ke kudancin kasar nan to za ku ga cewa marasa aurensu sun fi masu aurensu yawa, saboda wulakanta aure, in mace aurenta ya mutu ko mijinta ya mutu to ba wanda zai aure ta har mutuwarta.
Yanzu ga tambaya don a yi  alkalanci, a duk daurin aure 5 da aka yi a unguwarku shekara 2 da suka wuce nawa suka mutu a ciki? Ko kuma a unguwarku shin zawarawa da ‘yan mata su waye suka fi yawa kabilar a Hausa-Fulani? Sun zama tamkar zogale gandi mataimaki ana tsinkarka kana tsaye kana kallon jama’ar gari. Duk mutumin da ka ji yana aibata Hausa-Fulani a kan wani kuskure da suka yi, to ku tuntubi nasabarsa, wata kila akwai sirki a ciki.
Tabbas na yarda da cewa kabilata ta Hausa suna da saurin sakin aure a kan laifin da bai taka kara ya karya ba, babu shakka wannan saurin sakin aure da wasu suke yi ba karamin kuskure ba ne, amma kuma yana da kyau iyaye su rika taka rawa wajen yin sulhu tun kafin abin ya lalace, ya kamata ma’aurata su kai zuciya nesa, su rika hakuri da juna da kuma tausayi. A tuna Manzon Allah (SAW) ya umarci mazaje su kasance masu hakuri da tausayi a kan iyalinsu. Abu na karshe shi ne, ya kamata malamai da iyaye su ci gaba da fadakar da ma’aurata a kan hakuri da juriya da kuma tausayi.
 Wata magana mai kama da gaske wacce take yawo a bakunan mutane ita ce, a duk lokacin da mutum zai yi aure to ya fi matar abu 3; ta fi shi abu 3; su hadu a kan abu 3. Ma’ana, ya fi matar: karfi da Ilimi da kuma Kudi. Ta fi shi: Kyawu da Hakuri da Shagwaba, sannan su hadu a kan: Addini da Yare da kuma Gari daya.
A karshe idan aka yi la’akari da wadannan batutuwa za a gane matar Bahaushe sarauniya ce a gidan aure.
Ado Musa, unguwar kaura Goje, Kano 08069186916