✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rayuwar almajiran da suke karatu har zuwa jami’a ba tare da bara ba

A Najeriya musamman a Arewacinta idan ka yi maganar yara kanana masu karatun Alkur’ani ko allo wadanda aka fi sani da almajirai abin da zai…

A Najeriya musamman a Arewacinta idan ka yi maganar yara kanana masu karatun Alkur’ani ko allo wadanda aka fi sani da almajirai abin da zai zo wa mutane bai fi masu yawon bara ba.

Bara tana ci wa mutane da dama tuwo a kwarya, wanda hakan ya sa ake ta nazarin yaya za a iya kauce wa al’adar bara ga yara masu karatun allo.

A Jihar Sakkwato an samu mafita wadda za ta yi tasiri a iya magance wannan matsala, domin an gano akwai almajirai masu karatun allo da ba su yin bara a jihar.

– Yadda makarantar allon da ba a bara take

Ba kamar sauran makarantun allo, inda yara almajirai ke taruwa a gaban malami don su koyi karatu suke yi ba, ita Madarastul Hadimatul Islamiyya Wat-Tarbiyya wadda aka fi sani da Makaranyar Malam Umar Mai Hidima tana da nata tsari ba irin na sauran makarantun allo da almajiransu ke bara ba.

Makaratar Malam Umar Alhadim da ke Unguwar Mabera, Gidan Jariri a Karamar Hukumar Sakkwato ta Kudu a Jihar Sakkwato, ba ta bari yara su tafi yawon bara kan titi ko gidaje, kuma ana kawo yara daga dukkan kananan hukumomin jihar 23 da jihohin Neja da Zamfara da Kebbi.

Yanzu haka akwai dalibai sama da 2,000, kuma ana yi wa kowane dalibi rajista, sannan ana ajiye masa kudin magani sannan ana biyan kudin mako da sauransu.

A makarantar ba karatun allo kawai ake yi ba, har da na boko, kuma yanzu haka a makarantar akwai daliban da suka samu zuwa manyan makarantu da jami’o’i.

Yadda muke tafiyar da makarantar Shugaban Makarantar

“Ba mu daukar kowane yaro a makarantarmu sai iyayensa sun aminta za su samar da duk abin da yake bukata a wata.

“Wannan ba ya cikin kudin shiga makaranta Naira 4,000 da za a biya wa yaro, duk tsawon lokaci da zai dauka cikin makaranta biya daya ake yi”, inji mai makarantar.

Malam Umar Alhadim wanda shi ya kafa makarantar ya ce Naira 1,000 ne kudin rajistar shiga makaranta, 2,000 na yunifom, 1,000 za a ajiye ne a dakin magani dake kusa da makaranta koda za a samu ciwo na gaggawa tare da yaro a saya masa magani da kudin.

Malam Alhadim ya ce makarantar tana da dalibai 2,200 sannan sama da yara 400 ke kwana a wajensa.

Akwai kuma dalibai mata da ke zuwa lokacin karatu kawai, da an tashi sukan koma gidajen iyayensu; Ba su da wata daliba mace da ke kwana a makaranta don hakan ya saba wa karantarwar addini da al’dar Hausawa.

Shugaban ya yi wannan bayani ne lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya a harabar makarantar a ranar Talata da ta gabata, inda ya ce bai taba samun wata gudunmawa daga daidaikun mutane ko gwamnati ba.

Ya ce suna kula da makarantar ce daga kudin mako Naira 20 da dalibai ke kawowa, musamman wadanda ke yin tireda da dinkin hula da carbi da sauransu daga cikin daliban.

Kuma ya ce akwai lokacin da suke karbar Naira 200 daga dalibai amma yanzu rabin yaran kawai ke iya biya saboda matsin tattalin arziki da aka shiga a kasar nan.

Ya ce, “Mun fahimci ba alfanu mu bari har sai karshen wata. Ni da kanena ne da yake taimaka min muke tafiyar da makarantar don tabbatar da komai na tafiya yadda ya dace”.

Malam Umar ya ce makarantar tana karantar da ilmin addini ne, amma sun samar da ajujuwan karantar da yara boko a matakin firamare inda suke da fahimtar juna da wata makarantar firamare duk lokacin da suka yaye dalibansu makarantar ke ba da shaidar kammalawa daga nan yaro yakan tafi sakandare ya ci gaba da karatu har sai yadda hali ya yi.

Ya ce, “Muna da dalibai da dama a makarantun sakandare, akwai daya daga cikin yaranmu da yake rubuta jarrabawar kammala sakandare da ake kan yi yanzu.

“Shekara biyu da suka wuce dalibinmu ya samu nasara a darussa takwas cikin tara da ya rubuta a jarrabawar kammala sakandare, yanzu haka yana karatu a Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari a Sakkwato inda yake karatun Takardar Ilimi ta  Kasa (NCE).

“Kuma muna da yaron da ke karatu a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato yana karatun fannin Ilimi da Lissafi (Education Mathematics).

“Wadannan yara ba su tafi makarantar firamare ba karatun da muke koya musu ne ya wadatar da su har suka tafi sakandare.

“Ya kamata mutanen da ke kallon almajiri wani kaskantacce su sani hakan bai dace ba, domin wadannan yaran suna da basira da suke iya zama wani abu a rayuwa.

“Muna amfani da kudin makaranta mu biya wa wadansu dalibai kudin zuwa manyan makarantu domin mu kara karfafa musu gwiwa domin duk mahaifin da bai yarda dansa ya yi karatun boko ba nakan ce ya tafi da dansa ba mu daukarsa.

“Kuma wadansu iyayen na bukatar taimako shi ne dalilin biyan kudin makaranta ga daliban”, inji shi.

Ya yi kira gwamnati ta ba su gudunmawar kudi haka kungiyoyin masu zaman kansu, inda ya ce suna da malamai 11 a makarantar da tsofaffin daliban makarantar da ke taimakawa domin ba su iya daukar wadansu malamai daga waje.

Kuma ya yi kira ga gwamnati ta rika sanya dalibansa a shirye-shiryenta na koyar da sana’ar hannu.

Yadda na kai matakin jami’a Almajirin makarantar

Aliyu Umar dan Jihar Zamfara da ke karatu a Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo aji biyu, kuma yake karatun fannin Ilimi da Lissafi, dalibi ne a Makarantar Mai hidima.

Ya ce an kawo shi makaratar ce tun yana karami don ya koyi karatun  Kur’ani. A cikin haka ya ji sha’awar ya shiga karatun boko kan horarwar da malamin ke ba su.

Da ya kai wani mataki na karatun Alkur’ani ne sai ya shiga karatun, bayan kammala sakandarensa a Jihar Katsina ya yi karatun kwamfuta na wata uku kafin ya shiga jami’a.

Game da cewa ana ganin almajiri ba zai iya karatun boko ba, sai ya ce, “Gaskiya ba haka ba ne. Ya danganta da yaddda mutum ya dauka.

“Rayuwa na tafiya da tsari ne in ka sanya wa ranka za ka iya, shi ke nan. Karatun Kur’ani ba ya hana na boko, rashin yin karatun ga almajirai ya danganta ne da inda yaro ya tashi.
“Har yanzu wadansu na da gurguwar fahimta kan karatun boko. Bayan fahimta ta malami in malami bai yi ilimin zamani ba ta yaya zai ba wa abin muhimmanci tunda a wannan zamani sai an hada biyun”.

Umar ya ce, “Malam ne ke biya min kudin makaranta da wasu bukatun ilimi.

“Kuma kan karatun Kur’ani da na samu ban sha wahala a wajen gane karatun boko ba, hasali ma za ka ga duk wadanda ke shan wahalar karatun da muke yi suna da nauyin fahimta, musamman wadanda ba su yi karatun Alkur’ani ba kafin su shigo makaranta.

“Shi karatun Kur’ani mabudi ne in ka yi shi kwakwalwarka za ta bude, kuma za ta karbi duk abin da zai shigo” .

Dangane da burinsa a rayuwa, sai ya ce, “Burin da nake da shi bai fi in tsaya da kafafuna ba in taimaki ’yan uwana dalibai ta hanyar bude irin wannan makaranta don ba mai barin tushensa,” inji shi.

Za mu daga darajar makarantun allo a Sakkwato

Gwamnati

Babban Sakataren Hukumar Ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Jihar Sakkwato Dokta Umar Altine Dandin Mahe ya ce hukumarsa na kokarin daga martabar makarantun allo a jihar.

Dokta Dandin Mahe ya ce nan ba da dadewa ba za su gabatar da shirin “Sokoto B-tech Almajiri Model”, wanda ke nufin makarantun allo su tsaya da kafafunsu, inda shirin zai horar da malamai sana’o’i daban-daban bayan sun kware su zo su koyar da dalibansu.

Hakan zai sa su zama masu cin gashin kansu abin da zai iya rage bara a tsakanin almajirai.

Ya bayyana cewa suna da makarantun almajirai sama da 2,000 a Jihar Sakkwato