✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin tsoro da naci da jajircewa ne aikin jarida ke bukata – Sule Musa Dutse

Alhaji Sule Musa Dutse daya ne daga cikin ’yan jaridar da suka yi suna a aikin jarida, tun zamanin su Sa Ahmadu bello Sardaunan Sakkwato,…

Alhaji Sule Musa Dutse daya ne daga cikin ’yan jaridar da suka yi suna a aikin jarida, tun zamanin su Sa Ahmadu bello Sardaunan Sakkwato, Sule Musa yana daya daga cikin ’yan jaridar da suke da tasiri a Arewa, ya rike mukamai da dama ciki har da Daraktan Watsa Labarai na gidan gwamnati da Daraktan Ma’aikatar Watsa Labarai ta Jihar Kano. Wakilinmu ya zanta da shi kan yadda yake kallon aikin jarida a jiya da yau:

Yaya aka yi ka shiga aikin jarida?

A lokacin da aka kirkiro sababbin jihohi (a zamanin mulkin Gowon) Jihar Kano tana daya daga cikin jihohin da aka kirkiro, sai na nemi tafiya makarantar koyon aikin jarida da ke Legas wato Institute of Journalism domin na samu gogewa da kwarewa a fagen aikin jarida kasancewar ina son aikin a zuciyata. Allah Ya taimake ni na samu shiga makarantar kuma na samu tallafin karatu daga gwamnatin Jihar Kano.
A wancan lokacin akwai aminina marigayi Adamu Dutse wanda yake aiki da gidan rediyon BBC, lokacin yana karatu a London School of Journalism wato makarantar koyon aikin jarida da ke Landan shi ne ma ya biya min kudin makaranta na farko a shekarar da na gama na samu nasarar cin jarrabawata na samu kyaututtuka na fara neman aiki da ma’aikatar labarai ta Jihar Kano a 1970.
Me ya ba ka sha’awar shiga aikin jarida?
Lokacin da nake aiki a filin jirgin saman Malam Aminu Kano a matsayin daya daga cikin masu ba jirgi umarnin sauka da tashi ta hanyar sadarwa, sai hakan ya hada ni da manyan mutane irin su marigayi Malam Aminu Kano da danmasanin Kano Alhaji Maitama Sule. A wancan lokacin in na yi musu tambayoyi na rubuta labaraina sai na aika wa jaridar Daily Sketch a Legas, kuma ana sa labaran, wannan ya sa na fara gogewa a fagen watsa labarai da rubuce-rubuce, tun ba sa biya na har ta kai suna ba ni Dala uku zuwa Dala biyar a wancan lokacin a matsayin alawus. A kullum nakan samu labarai na aika musu daga baya na hada da jaridar New Nigerian su ma in na aika musu a wancan lokacin nakan samu kudin da ya kai Fam goma a matsayin alawus, kuma duk da haka ina samun albashina daga gwamnatin Jihar Kano na Fam 17 da sulalla. Ana haka har ta kai na rika zuwa gidan marigayi Malam Aminu Kano ina hira da shi. Na samu halartar kwasa-kwasai a fannin aikin jarida da dama wanda hakan ya ba ni damar da nake cin moriyar aikin har yanzu. Karatuna na karshe a fagen aikin jarida na yi shi ne a birnin Landan a 1983 inda na samu wata shida a can.
Wane kalubale ke cikin aiki jarida?
Aikin jarida ba ya bukatar tsoro yana bukatar mutum mai naci da jajircewa wajen tabbatar da sahihancin labarai da gabatar da su komai dacinsu, domin ya tabbatar da gaskiya a ko’ina take. dan jarida ba ya nuna kwadayinsa a fili domin zai yi hulda da manyan mutane da talakawa, shi na kowane ana bukatar dan jarida ya zama na kowa amma ya zama tare da masu gaskiya tare da fallasa marasa gaskiya. Tunda nake aikin jarida shekara 35 ba a taba ba ni takardar tuhuma ba. Kuma dan jarida ba ya girman kai sai aiki tukuru don taimakon jama’a wannan shi ne aikin dan jarida
Aikin jarida yana bukatar mutum mai kutsa kai ba rago ba, yana bukatar mutum mai kazar-kazar, domin aikin jarida ba na malalaci ba ne, rago ba ya aikin jarida.
Ko akwai mukaman da ka taba rikewa a baya?
A gaskiya na rike mukamai masu yawan gaske ciki har da Sakataren Watsa Labarai na gwamnoni uku. A Jihar Kano na yi zamani da Gwamnan Kanar Sani Bello a 1978 da kuma Iya Kwamanda Ishaya Shekari da kuma marigayi Abubakar Rimi. Na kuma taba zama Babban Jami’in Watsa Labarai na Jihar Kano wanda a yanzu ya fi mukamin Babban Daraktan Watsa Labarai, ina daya daga cikin ’yan kwamatin kirkiro Jihar Jigawa, kuma na taba zama sakatare a gidan rediyon Jihar Jigawa daga 1990 zuwa 1997. Godiya ta musamman ga Alhaji Ali Sa’adu Birnin Kudu wanda a matsayinsa na Gwamnan farar hula na farko ya yi matukar kokari wajen ci gaban Jihar Jigawa.
Wadanne nasarori ko kalubale ka fuskanta a aikin jarida?
Na samu nasarori wajen bayar da shawarwari ga daukacin gwamnonin da na yi zamani da su, kuma duk da cewar ina karami ne na samu nasara wajen bayar da shawarwari. Na samu nasarori masu yawa da takardun yabo har 12 daga kungiyoyi daban-daban da ma’aikatun gwamnati. An ba ni takardar yabo bisa kirkiro Jihar Jigawa, kuma na taimaka wa yara da dama wajen shiga aikin gwamnati da sauran ayyuka a kamfanoni, kuma ban taba da na sani ba wajan shiga ta aikin gwamnati da aikin jarida. Matsalar da na samu ita ce a lokacin ina sakataren gidan rediyon Jigawa zamanin Gwamna Ali Sa’adu da Kanar Ibrahim Aliyu sun hana ni damar da zan gudanar da aikina ta hanyar hana ni kudin da zan yi aikace-aikacen da suka kamata, hakan ya haifar min da bakin jini a tsakanina da ma’aikata.