✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin sabbin kudi ya sa an dakatar da bikin al’ada a Ile-Ife

Masarautar ta ce za ta sanar da ranar yin bikin a nan gaba

Karancin takardun kudi a hannun jamaa da matsalar man fetur da tsadar shi ta sa Fadar Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi daukar matakin dakatar da bikin alada na Aje da aka saba yi a masarautar Ife a Jihar Osun.

Ana yin bikin ne bisa al’ada a daidai irin wannan lokacin a kowace shekara.

Bayanin haka yana kunshe ne cikin wata takardar sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Fadar Sarkin, Otunba Moses Olafare ya sanya wa hannu ranar Laraba.

Sanarwar ta ce, “Mai martaba Ooni na Ife ya dauki matakin dakatar da wannan gagarumin biki na Aje ne domin tausayawa ’yan Najeriya da suka samu kansu cikin matsalar karancin takardun kudi a hannunsu da matsalar karancin man fetur da tsadar shi da sauran matsalolin da za su iya share hawayen jama’a.

Fadar ta kuma ce Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya bayar da umarnin daukar matakin ne bayan wani taro na musamman da ya yi da manyan fadawa da jagorar shirya bikin na bana, Iyalaje-Oodua da Gimbiya Dokta Toyin Kolade da dukkan masu ruwa da tsaki na masarautar.

Taron ya bayar da hakuri ga jama’a masu rububin ziyartar bikin na bana daga sassa daban-daban na ciki da wajen Najeriya.

Sanarwar ta tabbatar da cewa za a fadi ranar da za ayi wannan biki da zarar an kammala zaben kasa mai zuwa.

Ana gudanar da bikin na Aje ne a yankin Yarabawa musamman masarautar Ile-Ife ne domin nishadantar da jama’a da wayar da wayar da kansu.