Karancin takardun kudi a hannun jama’a da matsalar man fetur da tsadar shi ta sa Fadar Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi daukar matakin dakatar da bikin al’ada na ‘Aje’ da aka saba yi a masarautar Ife a Jihar Osun.
Ana yin bikin ne bisa al’ada a daidai irin wannan lokacin a kowace shekara.
- Kotun Koli ta dage sauraron kara kan canjin kudi
- An mayar da Kwalejin Sa’adatu Rimi da ke Kano matsayin jami’a
Bayanin haka yana kunshe ne cikin wata takardar sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Fadar Sarkin, Otunba Moses Olafare ya sanya wa hannu ranar Laraba.
Sanarwar ta ce, “Mai martaba Ooni na Ife ya dauki matakin dakatar da wannan gagarumin biki na Aje ne domin tausayawa ’yan Najeriya da suka samu kansu cikin matsalar karancin takardun kudi a hannunsu da matsalar karancin man fetur da tsadar shi da sauran matsalolin da za su iya share hawayen jama’a.
Fadar ta kuma ce Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya bayar da umarnin daukar matakin ne bayan wani taro na musamman da ya yi da manyan fadawa da jagorar shirya bikin na bana, Iyalaje-Oodua da Gimbiya Dokta Toyin Kolade da dukkan masu ruwa da tsaki na masarautar.
Taron ya bayar da hakuri ga jama’a masu rububin ziyartar bikin na bana daga sassa daban-daban na ciki da wajen Najeriya.
Sanarwar ta tabbatar da cewa za a fadi ranar da za ayi wannan biki da zarar an kammala zaben kasa mai zuwa.
Ana gudanar da bikin na Aje ne a yankin Yarabawa musamman masarautar Ile-Ife ne domin nishadantar da jama’a da wayar da wayar da kansu.