✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin bututun ruwa na damun garin Kude

Editan Aminiya, mai farin jinni, ka ba ni dama in mika kukan mutanen garinmu ga Mai girma Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji sule Lamido. Muna rokon…

Editan Aminiya, mai farin jinni, ka ba ni dama in mika kukan mutanen garinmu ga Mai girma Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji sule Lamido. Muna rokon Mai girma Gwamna da ya dube mu da idon rahama ya sa akawo dauki zuwa gyaran bututun ruka da aka sanya a layukan kofar Kudu da Layin Kasuwa. Don wadannan unguwanni na fama da matsalar bututun ruwa.
Da fatan Mai girma Gwamna zai duba wannan matsalar ta al’umma. Mun gode. Daga Idris Ibrahim 07058921124.

Sakonnin waya

Edita a kara hakuri
Jama’a ku dinga yi wa Editan Aminiya uzuri, yana kokari fa. Sannan kuma kaima Edita kasan hulda da jama’a dole sai ka yi hakuri. To don Allah ka kara hakuri da jama’arka. Mu dai sai dai mu yi ma addu’ar alkhairi. Allah Ya kara mana kaifin basira. Daga Sadi Khalid Jos 07033306067.

’Yan mata a koyi girki
Edita don Shugaban Ananbawa ka ba ni fili, in yi kira ga matasan’yan mata su rage girman kai su koyi girki a wurin kakanninsu. Domin sun fi duk wani gidana binci iya girki a kasar nan. Ko Edita ne ya ci girkin kakata, sai ya yi santi. Daga Zahra’u Auwal Sagagi Kano. 08095167032.

Ga Gwamna Lamido
Gaisuwa ga Gwamna mai adalci, Alhaji Sule Lamido. Allah Ya baka matsayi na gaba. Amin. Daga Mujtaba Adamu 08037783824.

Ga Gwamna Kwankwaso
Don Allah Aminiya ku mika min kokon barata ga Gwamnan Jihar Kano, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso. Yau shekara guda ke nan da aka dauke mana na’urar rarraba uwatar lantarki (Transformer), ba ita, ba labarinta. Mu jama’ar danmarke muna neman taimakonka, ya mai girma gwamna. Daga Kabiru Shehu Sarina 08038717417.

Martini ga Sale Zazzaga
Aminiya don Allah ku taimaka ku sanya mini sakonnin martini ga Alhaji Sale Zazzaga. Ka ce wai APC ba za ta iya kafa gwamnati a Najeriya  ba. Lallai ka nuna ma duniya cewa baka san komai ba. Ka shjirya yin fada da Allah (SWT). Saboda shi ke kafa mulki ba jam’iyya ba. Muna neman tsari daga sharrin masu gurgun tunani. Daga Surajo Suleja IBB Market. 07037780446.

Ga Shugaban Kwastam
Aminiya don Allah ina so ku ba ni dama in jinjina wa Shugaban Kwastam na kasa, wato Alhaji Abdullahi Dikko Inde, bisa namijin kokarin da yake yi, wajen ci gaban aikin kwastom, da ma kasa baki daya. Daga Suleiman Shehu Na-Allah Samaru Zariya 08058395167.

Ga Gwamna Wammako
Wammako muna da matsalar ruwa a Sakkwato. Kuma ka snai a duk Najeriya a Sakkwato ne kawai muke sayen rukwa Naira goma zuwa sha biyar, sannan mu sayi jakar ruwa Naira dari. Haba jama’a; sannan 2015 a kawo dan takara? Mu jahilai ne aka ce muku? A dai sake shawara. Daga Aliyu Sani 08189185516.

A daina kafirta juna
Assalamu alaikum. Zuwa ga Edita, don Allah ina so ka ba ni dama in yi kira ga manyan malamanmu da suji tsoron Allah, su daina kafirta juna; su gaya wa mabiyansu gaskiya, musamman a lokacin watan Ramadan. A tuna fa wata ne na neman lada. Daga Uban dalibai Ranchass 08052659678.

Shawara ga Editan Aminiya
Assalamu alaikum. Editan Amintacciyar jaridarmu ga shawara ta gareka. Ya kamata a mayar da shafukan Zinariya masu launi, musamman shafin adon mata. Ba ya kyau sam in babu launi, sai ya yi bakikkirin, kamar yadda bugun makon baya ya yi. Da fatan za a duba a gyara, don ta zama kamar sauran takwarorinta. Naku AbdulMumini Yahaya sheka 08038386842.

Aminiya ga lambar yabo
Mun ba Aminiya lambar yabo (Award).Kowa zai yi korafi a kan sakonni, sai ya ce wai sai na Katsinawa ake bugawa, to Aminiya dai ta kowa ce; sai dai Katsinawa sun fi turo da sakonni. Daga Aminu M. Mai’adua 07038243900.

Ga Gwamnan Babban Banki
Sanusi Lamido sanusi, ya kamata a kara yawan kananan kudi, kamar Naira 20 da 10 da 5. Saboda su ne mu talakawa muke harkokinmu nay au da kullum, kamar mu mutanen karkara, mun fi amfani da kananan kudi, wajen harkokin kasuwancinmu. Daga Isah Sani Mai Arsenal Garkon Alli, Jihar Jigawa 0702556844

Ta’aziyya ga Zamfarawa
Salam. Aminiya don Allah ku mika min ta’aziyyata ga mutanen Zamfara. Daga Abdul Usman CAC Abuja 0810706050.

Martani ga Sale Zazzaga
Sale Zazzaga ka sani duk isarka a PDP ba ka kai Yayale Ahmad ba; ba ka kai Bello Halliru ba; ba ka kai Wamako ba; ba ka kai Amaechi ba. Rana tsaka aka kore su daga PDP bare kai. Don haka ka kiyayi APC ikon Allah ne tafi karfinka. Daga Sani Abdu Beta 07068223015.

Bangajiya ga Sani zorro
Salam Aminiya ku ba ni dama in mika gaisuwa da kuma bangajiya ga Malam Sani zorro da ziyarar da yake kawo mana masarautar Gumel, da Gagarawa da Maigatari da Sule Tankarkar. Allah Ya saka da alheri. Amin. Daga 07030647958.

Ina zan samu Aminiya
Jinjina ta musamman ga jaridar Aminiya. Don Allah a ina zan rika samun jaridar a Fatakwal, Jihar Ribas. 07039336645.

Gaisuwa ga Aliero
Fatan alheri ga Aminiya, sakon gaisuwa ga tsohon Gwamnan Kebbi, Alhaji Dokta Muhammad Adamu Aliero. Daga Aisha Sani, Jihar Kebbi 08096961382.

Shugaban PDP ba si da farin jini
Assalamu alaikum. Aminiya a gaskiya a tarihin PDP ba mu taba shugaban Jam’iyyar dab a shi da farin kamar Bamanga Tukur ba. A gaskiya bai kamata a bar mana shugaban da ba shi da kishin al’ummarsa ba. Daga Alhaji Sale Zazzaga, Jos Bukuru, Filato 08144406080.

Ga fim industry
Wannan hukuncin da kuka yi wa Nafisa Abdullahi tamkar kara bayyana hadarin da ke industry dinku ne. Farkon shigowarta fim ai ba haka take ba, wato kun ci moriyar ganga ko? 08052244384.

Ga Shugaban karamar Hukumar Igabi
Godiya ga Alhaji Shehu Kwarau, Shugaban karamar Hukumar Igbi, a game da taimaka wa wasu marasa lafiya, domin yi musu tiyata. Dukkan wadanda suka samu wannan taimako Alhamdu-Lillahi, sun samu lafiya. Allah Ya sanya masu mulki su yi koyi da wannan kokari. Amin. Daga Maryam AbdurRasheed Jaji. 0702366792.