A inganta tsaron Najeriya
Harin bama-bamai da aka yi a Kaduna a Larabar mkon jiya, akwai lauje a cikin nadi, ya kamata gwamnatin tarayya ta inganta tsaro a cikin kasar, musamman ma Arewa inda aka maida yankin tamkar filin daga a kasashen Iraki, da Afghanistan. Daga Ishak Abdullahi dan Rimi Bena [email protected].
A daina ganganci
Bikin Sallah: Salam Edita Dan Allah ka ba ni dama na yi kira ga ‘yan uwa Musulmi musamman matasa idan lokacin bikin Sallah ya zo da su kauracewa duk wasu abubuwan da suka shafi shaye shayen kayan maye da kuma amfani da abubuwan hawa ana ganganci akan tituna hakika yin haka yasabawa Shari,a kuma hakan ba koyarwar Musulunci bace Daga Muhammad Aminu Baka noma Kano 08069735151.
An muzanta mata
Amfani da mata wajen kai hari ba karamar illa zai jawo wa matanmu na Musulmi ba, a Najeriya. Kuma muzanta Musulunci ne da Musulmi. Daga Isa Sani Mai Arsenal, Garkon Alli, Jihar Jigawa 08098556450/08072556844.
Jaje ga Tijjanawa
Assalamu alaikum Editan Aminiya ka mika min jaje ga Tijjanawa da faillawa kan ahrin da aka kai ma Sheikh dahiru Usman Bauchi da jagoran talakawa, Janar Muhammadu Buhar. Allah Ya kiyaye su. Mu kuma ’yan Arewa mu nemi mafitar wannan yaki da ake yi mana a wurin Allah. Daga Shehu Jinin Tukudu, Lafia, Jihar Nasarawa. 09036026384.
Ga Shekarau
Su Shekarau sun koma PDP, ga shi ana ta halaka mutane a Jihar Kano, kuma ba su8 ce komai ba, lallai mu tuhume su, kuma kada mu sake mu bas u damar jan ragamar wannan jihar nan gaba, don ba a san irin makircin da za su kulla ba. Allah Ya saremu da sharrin masu sharri. Daga Sani Ya Malam, Kano, Mazaunin Sakkwato 08126466663.
Barka da Sallah
Salam Aminiya, don girman Allah ku taimaka ku mika min gaisuwar sallah ga daukacin Musulumin duniya. Daga fatan an yi sallah lafiya.. Allah Ya karamana zaman lafiya a kasrmu Najeriya. Amin. Azzubair M. Fagge 08034412272.
Barka da Sallah
Assalam. ’yan Aminiya ina yi muku barka da sallah. Da fatan an yi sallah lafiya. Allah ya maimaita mana , cikin rai da koshin lafiya. Amin. Daga ’Yar mutan Bichi 08181862470.
Ga Sarkin Musulmi
Assalam Aminiya ina so ku ba ni dama in mika sakon taya murana ga Mai alfarma sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar da Sarkin KAtsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da Shugaban Jama’atu Izalatil Bidi’a wa ikamatus Sunna, Imam Abdullahi Bala Lau. Da fatan sun yi sallah lafiya. Daga Atiku Umar Katsina 08058408868.
A yi addu’a
Edita ka isar min da sakona a al’umma, musmaman ’yan Arewa, a duk sa’adda aka kammala ayyukan ibada, a rika tsayawa a yi addu’a. Allah Ya ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Allah Ya yi mana magani. Daga Khamis Bashir Gama 08030932677.
Addu’a ga Najeriya
Ya Allah ka kawo muna zaman lafiya a mai dorewa a yankinmu na Arewa da kasarmu Najeriya da ma Yammacin Afrika, baki daya. Daga AbdulMalik Sa’idu Mai biedi, Tashar Bagu Gusau.
Ga Al-Zakzaky da dahiru Bauchi
Ta’aziyya ga dan uwa Sheikh Ibrahim Al-Zakzaky a game da mutuwar zaratan ’ya’yansa uku maza! Ina jajanta wa Sheikh dahiru Usman Bauchi da Janar Buhari game da hari bama-bamai da ka kai musu ranar Laraba 23/7/14. Allah Ya kyaut ana gaba. Musulmi da Kiristoci da Maguzawan Arewa hattara. Daga Muhammad Kasim 08054018338.
Editan Aminiya mai jama’a. Don girman Allah ka ba ni dama in mika sakon barka da sllah ga Musulmin duniya, musamman ga Gwamna Shema da iyalan gidansa masu albarka, muna alfahari da ayyukanku. Gwamna ka yi taka, ka yi ta mai dan karfi. Mun gode. Daga Amiru Isa Bakori 08075959086.
Barka da sallah
Edita ka gabatar min da sakon barka da sallah zuwa ga ’yan uwa Musulmi. Da fatan an yi sallah lafiya. Daga Al-amin Artist Gama 07061863098.
Darussan Ramadana
A yau Ina so nayi amfani da wannan dama domin na taya al’ummar musulmin duniya murnar kammala azumin watan ramadana lafiya, da fatan za mu gudanar da bukukuwan sallah cikin wadata da kwanciyar hankali. Sannan kuma ina kira ga daukacin ‘yan uwa musulmi da mu dage mu ci gaba da amfani da darrusan da muka koya a cikin watan na ramadana. Allah ya amshi dukkan ibadun mu, ya kuma maimaita mana ta badin-badada. Ameen. Daga Abdu Bello Rishi, Dokta Alfanu e [email protected].
Ga Janar Muhammadu Buhari
Edita ka ba ni dama in mika sakon jaje ga janar Muhammadu Buhari. Daga karshe ina yi muku barka da sallah. Daga Masman Sanda dan Nijar Deidei, Abuja 07056991838.
Edita na yi laifi ne?
Wai don Allah Edita na yi maka laifi ne, ko dai sakona ya saba wa ka’idarka; Idan kuma ba haka ba ne, to mene ne dalili? Sati bakwai ban ga sakona ba, kuma duk sati sai na aiko. Ina fatan za a buga wannan, musamman zuwa ga shugabanni da malaman addini ina kira da su ji tsoron Allah. Allah Ya rufa mana asiri. Daga Muhamad dan Chiranchi, Deidei Abuja 08028984247.