✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha 2018: Kocin Eagles zai karbi tukuicin Naira Miliyan 10 a zagayen farko

Rahoton da wata kafar watsa labarin wasanni SCORENigeria ta fitar a shekaranjiya Laraba ya nuna Kocin Super Eagles Gernot Rohr zai karbi alawus din Dala…

Rahoton da wata kafar watsa labarin wasanni SCORENigeria ta fitar a shekaranjiya Laraba ya nuna Kocin Super Eagles Gernot Rohr zai karbi alawus din Dala Dubu 30 kwatankwacin Naira Miliyan 10 da dubu 800 idan kungiyar ta samu nasara a wasannin zagayen farko a lokacin gasar cin kofin duniya a Rasha.

Haka kuma rahoton ya nuna ’yan kwallon Eagles za su samu kyautar Dala dubu 15 ne kowannensu katankwacin Naira Miliyan 5 da dubu 400 idan suka samu nasara a wasannin zagayen farkon.

Najeriya dai za ta fafata a gasar cin kofin duniya a rukunin D ne da kasashen Ajantina da Kuroshiya da kuma Iceland.

Sai dai rahoton bai bayyana ko nawa kocin da ’yan kwallon za su samu idan suka yi kunnen doki a yayin wasannin ba.

A kwanakin baya ne dai NFF ta kara wa kocin wa’adin shekaru biyu ta kuma amince a kara masa albashin da yake karba na Dala dubu 50 kwatankwacin Naira miliyan 18 a duk wata.