✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha 2018: Ajantina da Fotugal sun tsallake rijiya da baya

  A ci gaba da fafutukar ganin kasashe sun haye gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a badi idan Allah Ya…

 

A ci gaba da fafutukar ganin kasashe sun haye gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a badi idan Allah Ya kaimu, a ranar Talatar da ta wuce ne kasashen Ajantina da kuma na Fotugal suka samu damar hayewa gasar bayan sun samu nasara a wasannin karshen da suka yi.

Ajantina wacce kafin wasanta da Ekuador take cikin tsaka mai wuya, ta samu damar hayewa ne bayan ta lallasa kasar da ci 3 da daya kuma shahararren dan kwallonta Lionel Messi ne ya zura dukkan kwallayen a raga.

Kawo yanzu kasar ce ta kasance ta uku a jerin kungiyoyin da ke fafatawa daga Kudancin Amurka.  Brazil ce ta farko sai Uruguay sai Ajantina sai Kolombiya sai kuma Peru.  Abin bakin ciki kasar Chile, watau kasar shahararren dan kwallo Aledis Sanchez na Arsenal ba za ta samu damar tafiya gasar ba bayan ta gama ne a matsayi na 6.

A Nahiyar Turai kuwa, a ranar Talatar da wuce shahararren dan kwallon Fotugal da kulob din Real Madrid na Sifen Cristiano Ronaldo ya taimakawa kasar hayewa gasar cin kofin duniya bayan sun lallasa Switzerland da ci 2-0.

Duk da yake dan kwallon bai samu damar zura kwallo ko daya a raga a wasan ba, amma yana daga cikin wadanda suka taimakawa kasar wajen ganin sun samu nasara a wasan.

Yanzu dai manyan kasashe irin su Faransa da Jamus da Ingila da Sifen duk sun samu damar hayewa gasar da za ta gudana a Rasha a badi idan Allah Ya kaimu.