Alhini
An nuna mini aikin hauni
Artabun zubar da jini
An zubar da rayuwar wani
An tsaya ana ta wuni-wuni
Rarakar rububin rudani
Rotsi da rauni
Rayuwa ta samu hautsini
Rudun rashin sani
Rashin riga da rawani
Batun ga akwai sarkakiya
babatun sasarin soyayya
Soyewar zukata ko kiyayyya
Kurtun Magana ya haifar da jayayya
Kisan wuka babu jinya
‘Yar bora
Ta rasa mamora
Salwantar da rai babbar asara
Tarin dami kan zabge da zara
Shi ya aka kai makura
’Yar mowa
A gidin murhu tana da uwa
Ta aza sanwa
Ta yi ta kwankwadar gahawa
Babu mai yi mata tsawa
Shi ma danlele
Ai ya yi male-male
Shishar dan malele
An bar mu muna ta kalle-kalle
daukar hankali da kyale-kyale
Marigayi dan Bello
Bibiyar kurtun halo alalo
Matarsa ta sha kallo
Sakonnin mata salo-salo
Sun yi tsiyakun karin kumallo
Labarai ne aka kalato
Jaridu ne suka ruwaito
Mahukuntan fuskantar boko
Tukin tuwon titin damun koko
Kowa ya sassauto
An bar aura ana jibgar taiki
Innar Mairamu ta hadu da masu baki
Wai babanta ne mutumin kirki
Alhali shi yai sakaci bayan saki
Sarayar da zuri’a ne rugujewar daki
Mace na da rauni
Miji ya zam da kaifin tunani
Ban da sakarci a sansani
Yasar da ta’adun iyaye da kakanni
Muna ta yi wa juna gani-gani
Yanzu masu taku da kulki
Sun bazama kan aiki
Bincike ne daki-daki
A daina kintace ba burki
Kada miya sai da maburki
Iyaye da ’ya’ya
Ku sauke wa kanku kaya
Hakkokin da suka rataya
A bayar da bayayya
A kiyayi tsiya-tsiya
A gurfana gaban alkali
Shi kuwa ya zamto adali
A yi hukunci na hankali
Kar a kyale mai fetali
keke-da-keke ai tozali
Cusa haushi
Ke haiufar da saurin fushi
Har a kai ga naushi
Da sukewar numfashi
Gaba babu fashi
Mu zamto masu da’a
Mutanen da ke kyautata dabi’a
Munanan ayyuka mu ce musu a’a
Kowa ya kiya yi masha’a
Mu daina yi wa juna ba’a
karshen makon da ya race an yi ta baza batutuewa bambarakwai kan kisan gillar dan Bello, wani matashi da ake ce mahaifinsa ya taba zama babban jigo a Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, kuma an yanke cewa mai dakinsa ce ta tsira mas tsitaka har ya ce ga garinku nan. Mafi yawan batutuwan dai a shafukan FUSKANTAR BOKOKO da na TUkIN TUWON TITI aka yi ta kwararo su, inda a kodayaushe akla zo sake jigba wa mai dakin dan Bello laifinm kisan gilla sai an Ambato mahaifiyarta, har ta kai ga ana ta nuni da cewa, mahaifint amutumin kirki ne, amma uwar ta yi hannun riga da ayyukan kwarai. Ni dai na fasko cewa, ‘mafi yawan al’amuran da aka ruwaito a kafafen sandarewar surutun sadarwa kawai RARAKAR RUBUBIN RUdANI ne.
Haurobiyawa matukar muna son tabbatar da adala sai mu tuhumi Mairamu da ta’asarta a kwanon tasarta, amma kada mu yi fafutikar mayar da ita ’YAR KUKA. Kuma ai shi ma mahaifinta wani katabus ya yi bayan ya sallama mahaifiyarta? To a bar kaza cikin gashinta; idan kuwa aka ci gaba da tone-tone to allura za ta tono garma,’ ta yadda masu laluben gararuma za su karke da gardama, a dinka mussu gumama su yi ta hauma-hauma.
Ina ganin bai dace mu yi ta ce-ce-ku-ce ba, musamman jin cewa masu taku da dan kulki dakon giwa tsagiya bugu da kari sun bazama wajen bincike, sai mu daina kawo musu tarnaki don su hanzarta wulwula takunb fedar keke, tunda su aka dora wa alhakin leke-leke, har a kai ga gaban alkali adali, wanda ba ruwansa da shafaffe da mai zanen fetali, har a tabbatar an yi keke-da-keke wajen tunkarar wannan matsala, inda daukacin masu ruwa da tsaki za su taho ai tozali.
Lallai a dainma shaci-fadi ko zantuttuka da yawan kaudi kamar rawar dodon kodi. Kuma na gargadi masu yada rade-radi, don gudun kada su haifar wa al’umma radadi. Wannan lamari ne na karon battar ’YAR MOWA da BORA
’Yan makaranta masu koyon watsattsake da buda wwagagen littattafai da mujallu da makalu da jaridu, babban abin nussarwa a wannan takammar kisan gilla da ake zargin Mairamu da salwantar da rayuwar danBello, shi ne daukacin wadanda ake ta RARAKAR RUBUBIN RUdANI a kansu, lallai duk miyagun dabi’un da suka bayyana wani ya aikata koda banker hayakin tabar SHISHA ce ko caka wa maigida TSITAKA har y ace ga garinku, mu yi kokarin kauce wa kwata mummmunan aikin da ya jefa jama’a cikin jimami ha rake ta alhinin zubar da jini, ta hanyar aikin hauni ko tsira tsinin tsitaka ta haifar da raunin da ya jawo jayayya ana ta kayya-kayya tun kafin a akai aya wajen gano yadda wannan matashi ya ce ga garinku ba tare da jinya ba. Haurrobiyawa mu yi kokarin tantance TSABA DA TSAKUWA, ta yadda kowa zai fasko masu yi mana kuwa suna daka wawa don mu rika yin tsuwwa.