Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya tsaya kai da fata cewa jirgin Nigeria Air mallakin Gwamnatin Tarayya zai fara shawagi kafin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bar mulki.
A cewar Ministan, jirgin zai iso Najeriya ranar Juma’a, kwana uku kafin Buhari ya bar mulkin.
- Kamfani ya kirkiro na’urar adana kayan miya su yi wata 3 ba su lalace ba
- Buhari ya bukaci Ministocinsa su ci gaba da zama a ofis har ranar rantsuwa
A baya dai Ministan ya sha fadin cewa komai ya kammala domin fara jigila da jirgin kafin karewar wa’adin Buhari.
Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, wacce wakilinmu ya kalla.
Ya ce, “Dangane da batun jirgin Nigeria Air, zai iso kasar nan ranar Juma’a a wani bangare na shirye-shiryen fara aikinsa.
“A ranar za mu kaddamar da jirgin wanda ke dauke da launin tutar Najeriya, kafin mu ci gaba da kwaso ragowar jiragen,” in ji shi.
A daren Talata, wakilinmu ya gano cewa akwai yiwuwar jirgin ya zao daga kamfanin Ethiopian Airlines, mallakin kasar Habasha.
To sai dai babu tabbacin ko kuma daga ranar jirgin zai ci gaba da shawagi ko kuma sai ya cika sauran ka’idoji tukunna.