Gaskiyar maganar Bahaushe da ke cewa: “Rana ba ta karya, sai dai uwar diya ta ji kunya”. Kamar jiya ne aka dage zabukan 14 da 28 ga watan Fabrairu zuwa makonni shida. Ga shi har makonnin sun kare. Ruwa ya kare wa dan kada, karya ta kare.
Alkalanci ya rage a hannun talakawa. Mu zabi canji daga rashin tsaro, ko ci gaba da zama a halin da muke ciki na rashin tabbas. Mu zabi canji daga tabarbarewar tattalin arziki ko ci gaba. Mu zabi canji daga cin-hanci da rashawa ko dauwama cikinsa. Mu zabi canji daga mulkin nuna wariya da kabilanci. Mu zabi canji daga rashin aikin yi da dimbin matasan Najeriya ke fama da shi. Mu zabi canji daga sace yan’mata. Mu zabi canji don samar da wutar lantarki. Mu zabi canji don farfado da mutuncin kasarmu a idon duniya. Mu zabi canji don ciyar da rayuwar mu gaba. Mu zabi canji don bayar da ingantaccen ilimi a makaratun gwamnati.
Daga Mansoor Sa’id
Jonathan ya raba kan Fulani
Me yake damun ’yan uwa Fulani da suka makance akan kudi wai Goodluck shugabanninsu za su zaba, amma nasan ban da mu talakawa.
Daga Muhammad Saeed
Tir da wadanda suka goyi bayan kungiyar Miyetti Allah Kaotal Hore wadanda suke da hannu kan nadin Shugaban kasa amatsayin shugabanta na dindindin.
Daga Mas’udu Meyi Bar
Musulmi sun yi Sallah a coci a Kaduna
Allah ya kyauta.
Daga Maryam Abdulaziz
To sai me?
Daga Sani Abdullahi
A coci kuma duk fadin garin Kaduna.
Daga Nuru S. Mahmoud
Babbar magana.
Daga Abba Ibrahim
Addu’ata da fatana…
Salam Editan, addu’ata da fatana shi ne duk wani ko wasu masu tarukan son kawo cikas ga zaben da ke tafe muna rokon Allah ya wargaza su ya kawo musu fargaba da matsala a rayuwansu. Allah ya taimaki Janar Muhammadu Buhari da mutanen kirki su yi nasara.
Daga Mudassir Ibrahim Mando, Jihar Kaduna, 08024122559
Mu zabi shugabanni nagari
Hakika komai ya bace hakuri ne babu. Yau cikin ikon Allah saura ‘yan sa’o’i al’ummar kasata Najeriya mu fito domin kada kuri’unmu ga shugabannin da muke ra’ayi. Saboda haka nake kara tunatar da ‘yan uwa yakamata mu fito domin zabar shugabannin da muke fatan za su magance mana matsalolin da suka addabi kasar mu Najeriya, musamman ma na rashin tsaro.
Daga Aminu dan-Kaduna Amanawa.
Bakin alkalami ya bushe
Salam, Shugaba Goodluck Jonathan bakin alkalami ya bushe, ka nuna ba ka san Arewa a fili karara sai da lokacin zabe ya gabato sannan ka nuna da muwarka ga yankin, mu kam anyi walkiya mun ganka, wannan ya nuna a fili ba ka iya mulkin jagoranci nagari ba, mukam sam a kai kasuwa mulikin Obasanjo da sauran da suka gabace ka duk ba haka suke tafiyar da ragamarba, ka nuna ba nuna fifiko ko watsi da wani bangaren, kai ko waye ma zamu iya zaba mu gwada sa’arsa, amma ba kaiba mara kishin kasa da rashin tausayin al’ummarsa.
Daga Hafizu Balarabe Gusau
Kira ga masu kada kuri’a
Zuwa ga Edita hakika yanzu kan muna cikin makon karshe da za mu tsaya mu kasa, mu tsaya, mu raka, mu jira har sai an ba mu hakkinmu na abin da muka zaba domin ita kanta Hukumar Zabe ta tabbatar mana da cewa muna da ikon mu tsaya mu raka mu jira inda babu wani tashin hankali da za’a kawo don haka matasan Najeriya mu yi amfani da wannan damar wajen neman hakkinmu domin kada ’yan baranda su yi mana magudi su dakushe mana fatar da muke yi na neman canji a fadin Najeriya baki daya.
Daga Usman Adamu Aliero, 07061594299.
Kira ga matasa
Assalamu Alaikum, Aminiya ku ba ni dama na yi kira ga ’yan uwana matasan Najeriya musamman na yankin Arewa da cewa kada farfaganda da kuma barazana da wasu ke yi mana, ya hana wasun mu fitowa ranar zabe domin kawar da mulkin kama karya, mulkin Sojan Dimukradiyya da jam’iyyar PDP ke yi mana shekara da shekaru.
Matasa kada mu sake da wannan dama da muka samu. Domin ta hanyan zabe ne kawai za mu iya kawar da gwamnatin da ba ta san ina ta dosa ba, domin a mulki na dimukradiyya zabe ne kawai ke iya kawar da gwamnati dun haka mu tambata babu wani da zai hana mu ’yancin mu nayin zaben gobe (Asabar).
Daga Ahmadu Manager Bauchi, 08065189242.