Ramin Tifa wani tafkeken rami ne da ke yankin Kuwait a Unguwar Tudun Murtala da ke Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano.
Ramin wanda ke da tsawon kilomita daya kuma yake da fadin kimanin mita 300 da kuma zurfin mita 500 ya zama wani tarkon mutuwa ga al’ummar yankin da sauran mutanen da ke wucewa ta wurin musamman baki wadanda ba su san cewa akwai rami a wurin ba.
Binciken Aminiya ya nuna cewa babu hakikanin yawan mutanen da wannan rami ya hallaka.
Ramin wanda mazauna yankin suka bayyana da cewa asalinsa fili ne na wani magidanci wanda a yanzu haka ’ya’yansa suka gada, tunda farko ana gudanar da sana’ar dibar yashi a wurin ne har zuwa yau.
Binciken Aminiya ya gano cewa mutanen yankin Kuwait sun yi kokarin ganin gwamnati ta kai musu dauki wajen hana aukuwar yawan mutuwar da ake samu ko kuma akalla a rage hadarin wurin ko kuma wucewa ta wurin, sai dai ba a samu cimma waccan biyan bukata ba.
Wata mazauniyar unguwar mai suna Malama Fatima Muhammad ta shaida wa Aminiya cewa da yawa mutanen yankin sun rasa rayukansu musamman ma yara inda ta danganta mutuwar da aljanu da aka ce sun yi kaka-gida a wurin.
A cewarta “Mutuwa dai ta zama ruwan dare a wannan wuri koyaushe, babu mutumin da zai iya gaya muku hakikanin yawan mutanen da suka rasa ransu ko kuma suka samu munanan raunuka a wannan wuri.”
Wani da yake jaddada abin da Malama Fatima ta fadi game da aljanu a kududdufin, Malam Haruna Sani ya shaida wa Aminiya cewa akwai lokacin da wata yarinya ta fada A kududdufin da aka tashi da safe sai ga gawarta ta yi sama, “Kin san abin da yake nuna cewa akwai aljanu a kududdufi shi ne idan aka samu gawa za ki ga an kwakwule mata ido an kuma turo ta saman ruwa. Irin hakan ta faru ba sau daya ba ba sau biyu ba,” inji Malam Haruna Sani.
Shi kuwa Malam Sa’idu Amadu ya shaida wa Aminiya cewa ne yawancin hadarin na aukuwa ne yayin da kananan yara suka je yin wanka a wannan kududdufi.
“Abin da yake faruwa yara suna nutsewa a cikin wannan kududdufi idan suka je wurin don yin wanka ko kuma irin wadanda suke wucewa ta gefen kududdufin a lokacin da suke tuka baburansu ko kekunansu musamman wadanda ba su san cewa akwai tafkeken kududdufi a wurin ba,” inji shi.
A cewar wani mazaunin yankin Malam Kabiru Usman sun yi kokarin katange kududdufin sai dai saboda katangar ta kasa ce ba ta dade ba, inda ya yi kira ga gwamnati kan ta gina katanga mai kwari don ceto rayukan al’umma. “Na san mutane masu yawa da suka rasa rayukansu a wannan kududdufi wadanda suka hada da masu keken mai kafa uku wadanda suka fada tare da dukkan fasinjojinsu.
Wasu gidaje da ke kusa da kududufin sun matse titin inda suka mayar da titin tsukakke wannan kuma shi ya kra ta’azzara halin da ake fadawa a ciki a yankin,” inji shi.
Alhaji Nuhu Muhmmad shi ne Mai Unguwar Kuwait ya shaida wa Aminiya cewa “Kudududfin ya samo asali ne daga Alhaji Yahya Gemu wanda ya sayi gona kimanin shekara 40 da suka gabata inda kuma ya mayar da wurin ya zama kududdufin da masu motocin tifa ke dibar kasa suna biyan lada don yin aikin gini da ita.”
Wani magidanci da ya rasa dansa ya shaida wa Aminiya yadda lamarin ya faru inda ya ce sun gane yaronsa nasa ya fada a kududdufin ne a lokacin da ya ga takalminsa a ajiye a gefen kududdufin “A takice wannan wuri zai kai kimanin shekara 40 a wancan lokaci babu gine-gine a kusa da kududdufin amma yanzu da yake akwai karuwar mutane za ka ga cewa akwai gine-gine kusa da wuirn inda ya zama hadari ga mutane ba wai kawai mazauna yankin ba har masu wucewa,” inji shi.
A cewarsa mutanen yankin sun ta yin kokarin gina katangar kasa sai da wannan ba isa ba. Ya kuma kara da cewa sun kai kukansu ga ga duk hukumomin da abin ya shafa sai dai har yanzu ba a kai ga samun mafita ba. “Kwanakin baya na samu labarin cewa wai wdanasu jami’an gwamnati sun zo wurin don dubawa amma da na bincika sai na iske maganar jita-jita ce domin babu ma mutumin da ya tuntube mu,” inji shi.
Wata da ta rasa dan uwanta mai kimanin shekara 13 a wannan kududdufi ta bayyana wa Aminiya cewa yaron ya yi sallama ya tafi makaranta sai gawarsa aka dawo da ita. Shi ma wani da ya rasa dansa mai kimanin shekara 17 a kududdufin, Salmanu Malam ya bayyana cewa ya yi iyakar kokarinsa wajen kafa kwamiti a yankin wanda zai magance wannan matsala sai dai bai samu taimakon da yake bukata ba. “Lokacin da na tabbatar cewa ba zan samu taimakon da nake bukata ba sai na kai maganar gidan jarida wannan shi ya janyo hankalin al’umma game da halin da wurin yake ciki. Sai dai abin da ya ba ni haushi shi ne maganar da mai unguwa ya fadi cewa wai mutane ne suka iske kududdufin ba shi ya iske su ba. Abin tambaya shi ne shin yana wakiltar mutane ne ko kuma yana wakiltar ramin ne?
“Magana ta gaskiya wannan wuri yana cin rayukan al’umma,” inji shi.
Sai dai dukkan mazauna yankin da suka tattauna da Aminiya sun yi kira ga gwamnati kan ta gagaguta kawo musu dauki don magance mutuwar mutanen yankin a cikin kududdufin.
Yayin da aka tuntubi Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kano, Daraktan Tsare-tsare da Bibiya na Ma’aikatar Dokta Garba Sale Ahmed ya bayyana cewa ma’aikatarsu ba ta samu wani korafi daga mutanen yankin Kuwait a hukumance ba kan kudududufin don haka ya yi kira gare su kan su rubuta wa ma’aikatar halin da ake ciki don daukar matakin da ya kamata.
A cewar Dokta Garba da zarar mutanen yankin sun rubuta kukansu ga Ma’aikatar Muhalli ita kuma za ta sanya jami’anta don duba wurin tare da kiyasta abubuwan da za a yi amfani da su wajen aikin katange shi ko abin da ya dace a yi masa. “Idan jami’anmu suka je wurin suka kawo mana abin da suka gani za mu tura ga gwamnati don daukar matakin da ya kamata,” inji shi.