Wani kwararren likita a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zariya, Dokta Sufyan Ibrahim, ya ce yin azumi a kai a kai na daya daga cikin sahihan hanyoyin magance Ciwon Suga nau’in type-2.
Ya kuma ce yin azumin na taimaka wa masu fama da cutar rage mummunar kiba da kuma sauran sinadaran da jiki ba ya bukata.
- Mutanen gari sun kashe dan bindiga a Kaduna
- Gombe da Kano sun yi nasara a musabakar Alkur’ani a Abuja
Likitan wanda ke jawabi yayin wata lakcar watan Azumin Ramadan da Kungiyar Likitoci Musulmai ta Najeriya (IMAN) ta shirya a Zariya ranar Juma’a, ya kuma bayyana azumin wata Ramadan da Musulmai ke yi a matsayin lokacin kara lafiya.
Ya kuma ce azumin na taimaka wa jiki wajen kone dukkan sinadaran da ba ya bukata, ta yadda garkuwar jikin dan Adam za ta samu daidaito da karin kuzari cikin ’yan sa’o’i da fara azumin.
Kwararren likitan ya kuma lura cewa azumi na taimaka wa kwayoyin halitta su yi aikinsu yadda ya kamata a jikin mai yin ibadar.
“Kazalika, yin azumi na rage fitowar wani kari a jikin mutum lokacin da ya fara tsufa, kuma yana dakushe cututtuka da dama,” inji shi.
Shi ma da yake nasa jawabin, Shugaban kungiyar ta IMAN, Malam Abdul’Aziz Hassan, ya ce su kan shirya lakcar ce a kowacce shekara da nufin wayar da kan mutane, musamman mambobinsu kan muhimmanci da kuma amfanin azumin Ramadan ga dukkan Musulmai.
Ya kuma ce kungiyar na da shirin ziyartar masu karamin karfi da marayu domin tallafa musu a cikin watan.