✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan watan alfarma da rahama Allah Ya sa mu dace

Ya ku wadanda kukai imani. An wajabta azumi akan ku kamar yadda aka wajabta shi akan wadanda suke gabaninku, tsammaninku za ku yi takawa-Suratu Bakara…

Ya ku wadanda kukai imani. An wajabta azumi akan ku kamar yadda aka wajabta shi akan wadanda suke gabaninku, tsammaninku za ku yi takawa-Suratu Bakara aya ta 183.
    Wannan aya ta sama na daga cikin ayoyin Alkur`ani mai tsarki da wasu Hadisan Manzon Allah (SAW) da suka wajabta yin Azumin watan Ramadan, da aka tashi da shi shekaranjiya Laraba, a zaman Azumin shekarar 1434, bayan da Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa`ad Abubakar  ya tabbatar da cewa Watan Sha`aban ya cika kwanaki 30 daidai a ranar Talatar da ta gabata don haka ya zama wajibi ga al`ummar musulmin kasar nan da su tashi da Azumin a ranar Larabar. Rahotanni daga sassa daban-daban na kasar nan sun tabbatar da cewa a bana an samu hadin kan akasarin musulmin kasar nana wajen daukar Azumin gaba daya, sabanin shekarun baya da kusan kowa ke yin yadda ta raya masa. Allah Ya sa yadda aka dauki Azumin kusan baki daya a cikin kasa, a kuma sauke shi baki daya cikin nasara da dacewar Allah SWT da ake fuskanta da Azumin, amin summa amin.
Azumin watan Ramadan farilla ne akan kowane musulmi da musulma masu lafiya wadanda kuma ba sa cikin tafiya. Kazalika yana daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar, sauran su ne fadin Kalmar shahada da aiki da abin da ta kunsa da Tsayar da Salloli guda biyar a yini da bayar da Zakkah (akan wanda ya mallaki abin yin Zakkar, wato kudi ko dabbobi ko amfanin gona) da zuwa Aikin Hajji ga mai iko.
A duk lokacin da aka ce irin wannan lokaci ya zo, bisa ga muhimmancinsa ga al`ummar musulmi a duk fadin duniya sukan shiga shirye-shirye ta fannoni daban-daban, na tunkarar watan. Wasu kan tanadi abinci da abin sha don iyalensu da `yan uwa da sauran al`ummar gari, wasu kan shiga hidimar sayen sababbin kayayyaki, don su kansu da iyalensu da `yan uwansu da ma na sadaukarwa kamar yadda wasu kan raba abinci danye ko dafaffe. Wasu ma ta kai sun matsar da rabon Zakkarsu ta kudi zuwa cikin wannan watan, duk dai da neman dacewa irin falala da rahamar dake cikin watan. Masu wadata kan tafi aikin Umrah, duk da neman dacewa akan Hadisin Manzo SAW dake cewa yin Umrah a cikin watan Azumin tafi lada, kuma da Azumin shi ne mafi soyuwa a wurin Allah SWT.
 A `yan shekarun nan na sama, wasu daga cikin gwamnatocin jihohin kasar nan (akasari inda musulmi suka fi yawa) sukan ware makudan miliyoyin Nairori wajen yin abincin buda baki don rabarwa a masallatai da makarantun Alkur`ani da wasu wuraren zaman jama`a, don buda baki ga mabukata. Wasu jihohin ma bayan irin wannan abincin buda baki, sukan ware miliyoyin Nairori, don sayen yadudduka da turamen atamfofi (har da kudin dinki)  da danyen abinci don rabawa ga talakawansu, kamar yadda Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ya ware Naira biliyan  a bana don raba irin wadannan kayayyaki ga talakawan jihar sama da 6,000! Gwamnonin da kan yi waccan dawainiyar ciyarwa da rarraba yadudduka da atamfofi, duk sukan yi da fatan Allah Ya kara kawo zaman lafiya kwanciyar hankali da karuwar arziki a jihohinsu da kasa baki daya     
   Watan na Azumin ya kan zama watan karatun Alkur`ani mai tsarki, walau ta tafsirinsa ko ta tilawarsa koma neman hardacesa. Akwai kuma karance-karancen littafan addinin Islama iri-iri da jama`ar musulmi kan dukufa wajen yi, bayan korarin yawaita sadaka da kyauta da sada zumunci, da  sallolin nafilfii iri-iri da ake yawaitawa dare da rana, duk da fatan dai a dace da rahama da gafarar da Allah Ya yi alkawarin yi wa bayinSa managarta a wannan watan.
Allah Ka sa mu dace  da rahamarKa da gafararKa da Ka yi alkawarin yi wa bayinKa a cikin wannan wata mai alfarma. Maluma na karantar da mu cewa a cikin watan Ramadan ne kawai Allah Ya ke rufe kofofin wuta Ya bude na aljanna Ya kuma daure shedanu, atakaice dai, wata ne da ya kamata musulmi ya koma ga Allah sau da kafa cikin tsoronSa da kwadayin rahamarSa, fiye da kowane lokaci, don kuwa ana nunnunka wa musulmin da suka mika wuya ladar ayyukan alherin da suka yi a cikin watan. Allah Ya sa mu dace.
   Maluma sun tabbatar da cewa Azumi ya akan zama garkuwar musulmi, ta hanyar hana ci da sha da jima`i  da yasassar magana da yi da mutane da haddasa husuma a lokacin da musulmi yake Azumi, har ma suna karawa da cewa, idan kana Azumi wani ya zageka, to kai kar ka rama ka ce da shi ‘Ni ina Azumi.’ Amma dukkan wadannan falala da garabasa dana ambata da wadanda ban iya ambatawa ba, da ake iya samu a cikin watan Azumi, duk ba sa samuwa sai idan an yi Azumin a bisa yadda Manzo SAW Ya koyar. A takaicen takaitawa dai wannan watan, wata ne da ya kamata kowa ya jajirce ya yi iyakacin iyawarsa wajen ganin ya koma ga Allah kuma komawa ta hakika. Allah don girman zatinKa da tsarkakarKa da IzzarKa Ka sa mu dace, Ka hada ayyukanmu da karba. Maraba da watan Ramadan watan Alfarma da Rahama.