La’akari da cewa azumi lokaci ne da ba a ci ko sha tsawon rana, mutane kan takaita ko ma su gujewa yin wasu ayyuka da ke bukatar amfani da karfi.
A wananan shekara da azumin ya zo a lokacin zafi wanda ake tsananin rana, masu azumin kan nemi wuraren da ke da inuwa su makale don gujewa zafin ranar wanda ka iya haifar musu da matsananciyar kishirwa.
- NAJERIYA A YAU: Ko watsi da tsarin karba-karba zai kai PDP tudun mun tsira?
- “Za mu kashe fasinjojin jirgin kasa idan gwamnati ta ki biya mana bukatu”
Sai dai lamarin ba haka yake ba ga masu gudanar da sana’ar da ke bukatar amfani da karfi kama daga ’yan dako da masu aikin gini da leburori da sauransu, domin yanayin sana’arsu ba zai ba su damar gudanar da aiki a inuwa ba.
A ziyarar da Aminiya ta kai wasu kasuwannin Jihar Kano, ta iske masu sana’ar dako suna gudanar da ayyukansu kamar yadda suka saba, inda yawancinsu suka bayyana cewa suna shan lemukan da ke kara kuzari.
Ya’u Saminu, dan dako ne da ke gudanar da sana’a a Kasuwar ’Yankaba a Jihar Kano, ya shaida wa Aminiya cewa duk da zuwan azumi, yanayin aikinsa bai canza ba domin yana fitowa da sassafe zuwa kasuwa don gudanar da sana’arsa kamar yadda ya saba.
Ya ce, “A gaskiya duk da zuwan azumi ban samu wani canji na aiki ba domin na kan fito da sassafe, kasancewar masu sayen kayan miya suna shigowa kasuwar da wurwuri, to a wanann lokacin za mu yi aikinmu sosai.
“Idan rana ta yi sosai idan babu aikin sai mu koma inuwa mu dan zauna don mu huta. Amma fa wannan ba ya nufin idan muka sami aiki ba za mu tashi ba. da zarar mun sami aiki za mu je mu yi komai tsananin rana kuwa,” inji shi.
Shi ma wani dan dako a kasuwar Singa da ke Kano mai suna Ibrahim Sani, ya ce duk da tsananin rana da ake yi a wannan lokacin, a haka yake fitowa domin ba shi da wata sanar da ta fi wacce yake yi.
“Idan ba mu yi wannan sana’ar ba to me za mu yi? Duk da aikin karfi muke yi, haka nan muke yi ba dadi, sai dai hakuri kawai.
“A rana zan tura kura cike da kaya daga Singa zuwa cikin Kasuwar Sabon gari ba adadi, ya danganta da yawan aikin da aka samu a ranar.”
A cewarsa, idan aka yi buda-baki, yana shan lemo mai sinadarin karin karfi a ciki domin karfin da ya rasa ya dawo.
Haka kuma ya ce yana shan ruwa sosai.
Shi kuwa Habu Adamu, wani magini ya shaida wa Aminiya cewa su kan gudanar da ayyukansu da sassafe yayin da rana ta yi sosai kuma sai su huta kafin daga bisani su ci gaba.
“A gaskiya a wannan lokaci na azaumi idan muna da aiki muna fita da sassafe don mu yi aiki sosai kafin rana ta take.
“yayin da muka ga rana ta yi sosai to mu kan dan sami wuri mu zauna mu huta domin gudun shiga matsala. yayin da rana ta dan yi sanyi sai mu tashi mu ci gaba.
“Amma fa aiki a wanann lokaci sai mutum ya daure duk da cewar wanann ita ce sana’ar da muka saba yi a kodayaushe.”
Shi ma wani da ke sana’ar sauke kaya a kasuwar Kantin Kwari, Magaji Bazamfare, ya shaida wa Aminiya cewa babu abin da suka daina na ayyukansu, duk kuwa da cewa suna azumi.
“Mu azumi ba ya hana mu gudanar da aikinmu. Wanan shi ne lokacin da muke samun kudi saboda mutane suna shigowa kasuwa sayen kayan sallah. Hakan ya sakullum a aiki muke.
“Mu farin ciki muke yi ma da aikin da muke yi don haka ma ba mu damuwa da azumi da zafin rana. Duk aiki da wahalar da muke sha ba mu damuwa da ita idan muka tuna kudin da za mu samu mu kan ji dadi sai mu samu karfin gwiwar yin aikin,” inji Bazamfare.
Ya kara da cewa ba ya wasa da shan magunguna na samun iarfi da maganin rana.
“Gaskiya abin da nake yi shi ne na kan sha magani sosai na samun karfi. haka kuma na kan sha maganiin rana. Kuma idan muna aiki na kan sami ruwan sanyi ko kankara na zuba a jikina domin na sami saukin zafin rana.”