A daidai lokacin da aka fara azumin watan Ramadan a karshen makon da ya gabata, Musulmai a sassa daban-daban na duniya na shafe tsawon sa’o’i daga lokacin sahur zuwa buda-baki.
Sai dai tsawon lokacin da kowacce kasa take shafewa tsakanin lokutan ya sha banban daga kasa zuwa kasa.
- ‘Dakatar da Sheikh Nuru Khalid ba zai hana mu fadin gaskiya ba’
- Gwamnati ta ba da umarnin toshe duk layukan wayar da ba a hada da NIN ba
Alal misali, akwai kasashen da ke yin azumin na tsawon sa’a 11 kacal, wasu kuma kan shafe kusan awa 17 ba ci, ba sha.
Kasashen da suka fi karancin sa’o’in yin azumi sun hada da New Zealand da Argentina da kuma Afirka ta Kudu, wadanda suke yin azumin awa 11 zuwa 12 kacal a kullum.
A gefe guda kuma, Musulman da ke birnin Reykjavík na kasar Iceland, su ne za su shafe lokaci mafi tsawo na azumi a bana.
Za su yi azumin ne na kusan awa 16 da mintuna 5 a kullum.
Akasarin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da na Yammacin Afirka dai a bana na shafe tsakanin sa’a 14 zuwa 15 yayin azumin.
Ga wasu daga cikin biranen duniya da adadin sa’o’in da suke azumi a cikinsu:
Johannesburg, Afirka ta Kudu: Awa 11 zuwa 12
Buenos Aires, Argentina: Awa 11 zuwa 12
Cape Town, Afirka ta Kudu: Awa 11 zuwa 12
Christchurch, New Zealand: Awa 11 zuwa 12
Ciudad del Este, Paraguay: Awa 11 zuwa 12
Montevideo, Uruguay: Awa 11 zuwa 12
Brasilia, Brazil: Awa 12 zuwa 13
Harare, Zimbabwe: Awa 12 zuwa 13
Reykjavík, Iceland: Awa 16 hours da minti 50
Warsaw, Poland: Awa 15
Landan, Ingila: Awa 15
Paris, Faransa: Awa 16 zuwa 17
Lisbon, Portugal: Awa 15 zuwa 16
Athens, Greece: Awa 15 zuwa 16
Beijing, China: Awa 15 zuwa 16
Washington DC, Amurka: Awa 15 zuwa 16
Ankara, Turkiyya: Awa 15 zuwa 16