Tambaya: Daga Yusuf M.K: Wadanne irin abinci ne suka dace a ci lokutan buda-baki da sahur?
Amsa: Malam Yusuf kai kana ma da zabi ke nan. Ai in fada maka yawancin al’umma ba su da wani zabi a bana sai dai abin da ya samu kawai, domin mu ma muna ji kuma muna bibiyar halin da ake ciki.
- Me ya sa ’yan mata ke jure talaucin gidan iyayensu, ban da na mazajensu?
- Bakin Balarabe: Bakatsinen da ya je Babban Taron APC na Abuja a kan rakumi
A yanzu a babban masallacin unguwarku wataqila zai yi wuya a samu ranar da ba a zo an yi barar abinci ko ta kudi ba.
Amma kai tunda kana da zabi ba abin da zai hana a fada maka. A yanayi na zafi, wanda kan sa ruwan jikin mutum saurin karewa ta hanyar zufa, dole mai azumi ya nemi abu mai ruwa-ruwa, kuma
sai ya guji rana.
Sa’annan da zarar an kai azumin bayan an tauna wani abu mai saurin dawo da sukari a jini kamar dabino ko dan abin da ya samu, sai a fara kokarin mai da
ruwan jikin.
Fa’idar dabino ita ce yana da sinadaran sukari kusan har nau’o’i hudu (glucose da sucrose da fructose da maltose),
wadanda jiki ke bukata kuma wadanda za su fara aiki nan da nan ba sai jiki ya sarrafa ba.
Har ila yau, akwai sinadarai irin su potassium mai kara karfin mommotsa jiki da na iron mai kara jini.
Wajen mai da ruwan jikin, shi gundarin abin bude-bakin zai fi kyau ya zamo mai ruwa-ruwa, duk wanda ran mutum ya ji ya fi bukata (mai sanyi ne ko mai zafi)
dangane da yanayi.
Abin da dai mutum ya ji zai iya sa hanjinsa ya ware, ba wanda zai sa ciki ya yi kabe-kabe ba, ya cushe, domin wannan wadansu kunu ko kamu ko shayi ya fi warware musu hanji, kafin daga bisani su dora wani abu, wadansu kuma abu mai sanyi makoshinsu ke bege, duk da dai watakila bai kai abu mai zafi ware ciki ba.
Don haka sai mutum ya duba ya ga wanne ne idan ya sha nan da nan zai ji ya bi jiki, bai zauna masa a ciki ba. Ba dai a so a take ciki tashi guda.
Can an jima idan aka zo cin abinci sosai, yana da kyau a kara yawan abinci mai gina jiki irin su kifi ko naman kaza ko na dabba da aka samu, ko iwai ko madara
ko awara ko kosai da ire-irensu, gami da masu kara kuzari irin su shinkafa ko tuwo da burabusko da sauransu, a ci daidai misali, har da ma masu sa jiki tara kitse irin su man shanu ko kakide ko bota duk a wannan yanayi za a iya tabawa.
Idan aka yi sahur kuma kada a kwanta bayan Sallah kai-tsaye sai an kara awa biyu haka ciki ya dan fada kafin a kwanta, domin kada mutum ya tashi da safe da kumburin ciki da kwarnafi.