Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi ta ayyana yau Laraba, 22 ga watan Fabrairu, 2023 a matsayin ranar 1 ga watan Sha’aban shekarar 1444 Hijiriyya.
Wata daya cur ke nan ya rage a shiga watan Ramadana, wanda a cikinsa Musulmi ke shafe wata guda suna azumin farilla da kuma jajircewa wajen gudanar da ayyukan ibada domin neman kusanci da Allah.
- Yau Kotun Koli za ta ci gaba da shari’a kan wa’adin tsoffin kudi
- Karancin kudi: An kona bankuna 10 rana guda a Ogun
Sanawar da Sakataren Kwamitin Ganin Duban Wata na Fadar Sarkin Musulmi, Yahaya M Boyi, ya fitar a ranar Talata baayn cikan watan Rajab kwanta 30 ta ce, Fadar Sarkin Musulmi ta ayyana ranar Laraba, 22 ga Fabrairu, 2022 a matasyin ranar 1 ga Sha’aban 1444 Hijiriyya.
Ramadan shi ne wata na tara a kalandar Musulunci, wanda kuma da zarar an kammala shi ake bikin Karamar Sallah.
A cikinsa na aka saukar da Al-Kur’ani a cikin Daren Lailatul Kadar, don haka Musulmi kan yawaita yin karatun Al-Kur’ani da sauraron tafsirinsa a cikinsa, baya ga sauran ayyukan ibada kamar Sallar Dare da kuma yawaita kyauta da sadaka da kuma kyautata mu’amala.
Bisa dukkan alamu, azumin watan Ramadan na bana a Najeriya zai kasance kwanaki kadan bayan babban zaben 2023, gabanin rantsar da sabuwar gwamnati.
Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, wanda shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci takan sanar da kwanakin watan Musulunci a kowane lokaci da nufin samun daidaito, musamman wajen aiwatar da ayyukan ibada da ke da kebabbun lokuta.
Wadannan sun hada da lokacin azumin Ramadan, Karamar Sallah, Babbar Sallah da kuma azumin ranakun tsakiyar watan Musulunci, wato ranakun 13 da 14 da kuma 15, ga masu son yi.