✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ramadan: An ga watan azumi a Saudiyya

Hakan dai na nufin ranar Asabar ce za ta kasance daya ga watan Ramadan

Rahotanni daga kasar Saudiyya sun tabbatar da ganin jinjirin watan azumin Ramadan na bana a sassa daban-daban na kasar ranar Juma’a.

Hakan dai na nufin ranar Asabar ce za ta kasance daya ga watan Ramadan na shekarar 1443 bayan Hijira, wacce ta yi daidai da biyu ga watan Afrilun 2022.

Hakan na zuwa ne bayan watan Sha’aban ya cika kwana 29, inda dama watannin Musulunci ba sa wuce kwana 29 zuwa 30.

Al’ummar Musulmai a fadin duniya dai kan azumci tsawon Ramadan, wanda shi ne wata na tara a kalandar Musulunci, inda suke kaurace wa ci da sha da kuma saduwa da iyali tun daga fitowar rana har zuwa faduwarta.

Kazalika, azumi na daya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci guda biyar.

A halin yanzu dai a Najeriya ana jiran sanarwa daga Fadar Sarkin Musulumi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, game da ganin watan na Ramadan.