Yin azumi a watan Ramadan na daya daga cikin rukunan Musulunci guda biyar kuma yana da amfani iri-iri ga Musulmai.
Baya ga ibadar azumin ita kanta, Ramadan wata ne da Musulmai a duk fadin duniya ke dada yawan ibadunsu domin neman kusanci da Allah da kuma neman gafararsa.
Kasancewar Musulmai na azumtar dukkan watan, dole akwai kalubalen da yake zuwa da shi, musamman game da abubuwan da suke lalata azumin, da wadanda ba sa lalata shi.
Aminiya ta yi nazarin wasu abubuwan da suke lalata azumi, ga kuma biyar daga cikinsu:
-
Ci ko sha
Duk wanda ya ci abinci ko ya sha abin sha da rana da gangan a watan Ramadan, to azuminsa ya karye.
Hakan kuma ya kunshi duk wani abinci ko na sha da ya shiga ta hancin mutum har ya kai ga shiga cikin mutum.
-
Yin jima’i/saduwa
Duk wanda ya yi jima’i da mace da rana a watan Ramadan, shi ma azuminsa ya karye. Wannan dai na daya daga cikin manyan hanyoyin karya azumi wanda ke dauke da hukunci mai tsanani.
Domin yin kaffara ga duk wanda ya karya azumi ta hanyar yin jima’i da rana, dole sai ya ’yanta bawa. Amma idan ba shi da ikon yin hakan, zai yi azumi 60 a jere, idan kuma ba zai iya yin hakan ba ma, to sai ya ciyar da miskinai 60.
Kazalika, duk wanda ya fitar da maniyyi sakamakon sumbantar mace, taba ta, shafa ta, ko kuma kowace irin mu’amala da jinsin da ba nasa ba, azuminsa ya karye.
Amma idan mutum ya fitar da maniyyin yana barci sanadiyyar yin mafarki, ko kuma kowanne yanayi da ba da gangan ba, to azuminsa bai karye ba. Fitar maziyyi ma ba ya karya azumi.
-
Yin kaho
Duk wanda aka yi wa kaho domin cire mataccen jini daga jikinsa alhali yana azumi, to azumin nasa ya karye.
Hakan dai na da madogara ne a wani Hadisin Annabi Muhammad (S.A.W) wadan Abu Dawud ya rawaito mai lamba 2367.
Bugu da kari, wannan hukunci ya kuma shafi wanda ya bayar da gudunmawar jini; ga wanda ya bayar da kuma wanda aka kara wa.
Sai dai ko da mutum ya rasa jini mai yawa sakamakon cire masa hakori, yin habo ko kuma jin rauni, azuminsa bai karye ba.
-
Yin amai da gangan
Duk wanda ya kakalo tare da yin amai da gangan alhali yana azumi, to ya lalata azumin nasa.
Amma idan ba da gangan ya kakalo aman ba, da kansa ya zo, azumin bai karye ba.
Hakan dai ya tabbata ne a wani Hadisi inda Annabi (S.A.W) ya ce, “Duk wanda amai ya zo masa, to ba sai ya rama azuminsa ba, amma duk wanda ya kakalo azumin da gangan, to ba shi da azumi, sai ya rama,” kamar yadda Tirmizi ya rawaito a Hadisi mai lamba 720.
-
Yankewar jinin haila ko na haihuwa
Idan jinin al’ada ya yanke wa mace, ko da ana dab da bude-baki ne, to azuminta na ranar ya karye.
Amma idan ta ga alamun lokacin jinin ya zo, amma ba ta ga jinin ba, to azuminta na nan.
Kazalika, idan jinin mace ya dauke da daddare, sannan ta yi niyyar yin azumi kashegari amma ba ta samu yin wanka ba kafin ketowar alfijir, malamai sun ce azumin nata na nan.
Sai dai kafi kowanne daga cikin abubuwa biyar din nan da aka lissafa a sama su karya azumi, dole su kasance da gangan aka yi su ba bisa kuskure ba, kuma ba bisa mantuwa ba, sannan a karan kansa ya yi, ba tilasta masa/mata aka yi ba.