✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rahoton Majalisar Dattijai game da kisan mutane a Apo

Daga yadda Majalisar Dattijai ta bayar da rahotonta game da kisan mutane takwas da jami’an tsaro na farin kaya (SSS) suka yi a unguwar APO,…

Daga yadda Majalisar Dattijai ta bayar da rahotonta game da kisan mutane takwas da jami’an tsaro na farin kaya (SSS) suka yi a unguwar APO, Abuja; a ranar 20 ga Satumba, 2013, lallai alamu sun nuna ko dai ba su fahimci yadda al’amarin ya faru ba ko kuma an binne lauje a cikin nadi; musamman ma ganin yadda kwamitin ya dauki dogon lokaci, ba tare da ya bayyana rahoton nasa ga al’umma ba. Abu ne mai kyau a ce kwamitin ya fahimci dukkan al’amuran da suka faru wajen kashe ’yan ci-ranin, domin kuwa hakan zai bayar da darasi a nan gaba. Kwamitin Sanata Mohammed Magoro ya wanke jami’an tsaro daga laifi, sannan ya kawar da ido daga zargin da su SSS suka yi da farko, da suka ce gidajen biyu da suka bude wa wuta, duk ’yan Boko Haram ne ke zaune a cikinsu.
Rahoton kwamitin ya tabbatar da bayanin da ke cewa, mafi yawa daga mutanen da ke zaune a gidajen biyu na Apo, leburori ne da ke aikin karfi da direbobin Keke-Napep. Akalla dai mutane sama da 100 ke zaune a gidajen, wadanda aka bude wa wuta da dare, aka harharbe su, a yayin da suke fitowa da gudu domin ceton rai.
Haka kuma, rahoton ya kara tabbatar da cewa lallai mutanen da aka harbe a cikin wadannan kangayen gidaje, leburori ne ’yan ci-rani, wadanda ke rakube a gidajen da sunan makwanci. Haka kuma, sun nuna cewa kisan da aka yi wa mutanen takwas, ba za a kira shi da ‘kisan kai’ ba amma dai za a iya kiran abin da SSS suka yi a matsayin ‘wani aiki da aka gudanar cikin gaugawa.’ Irin yadda rahoton nan ya wanke jami’an tsaro daga laifin kisan mutanen nan, abu ne mai matukar ban mamaki. Kodayake wasu daga cikin ’yan kwamitin na Magoro, sun alakanta rahoton a matsayin ‘mai wanke masu laifi.’ Akai kuwa kanshin gaskiya ga batun nasu.
Abin da kwamitin ya gano game da abin da jami’an tsaron suka aiwatar a ranar 20 ga Satumba, 2013 shi ne, sun yi kisan kai, amma dai bai fadi haka karara ba a cikin rahoton, wanda haka ke nuna cewa lallai akwai tsambare a binciken nasu.
Kamar yadda bayanai suka gudana na yadda al’amarin ya faru, babu wani dalili da zai sa jami’an SSS su yi abin da suka yi a Apo. Koda a ce ma an samu tabbacin wadanda ake zargin ’yan Boko Haram ne, bai kamata a kashe su ba tare da an bi hanyoyin da shari’a ta tanadar ba.
Majalisar Dattijai tana kokarin ta wanke SSS daga laifin kisan kan da ake zargin sun aikata, duk kuwa da cewa hujjoji karara sun bayyana a rahoton kwamitin na laifinsu. A haka kuwa, ba su yi wa kansu adalci ba, domin kuwa al’umma da dama za su sanya rahoton nasu cikin zargi, ganin cewa yana da gibi. Faruwar hakan kuwa na gaskata rade-radin da aka rika bazawa, cewa akwai wasu hamshakai daga Majalisar Dattijai, har ma daga Fadar Shugaban kasa da aka yi zargin cewa sun uzura wa kwamitin cewa kada ya sake ya alakanta laifi ga jami’an tsaron game da kisan mutanen na Apo. Ana zaton ma cewa, jinkirin da aka samu na fitar da rahoton, yana da alaka da irin wannan uzurawa.
Yadda jami’an tsaro suka yi ta jerangiya da bayanai na kariya, bayan aika-aikar da aka tafka a Apo, alamu suka nuna cewa za a binne gaskiya. Misali, maimakon SSS su amsa cewa sun yi kuskure, sai suka bige da cewa wai an bude masu wuta daga gidajen da mutanen ke zaune. Haka kuma, ba su nuna wani makami ko albushin da suka samu a gidajen ba. Majalisar Dattijai kuma ta nuna amincewa da batun jami’an tsaron, da suka ce ai sun samu labarin sirri ne cewa ’yan Boko Haram na shirin kai wa wurare daban-daban a Abuja farmaki. Babu wata shaida da aka gabatar ko ta na’ura ko ta takarda da ta tabbatar da samun irin wannan labari na sirri.
Kwamitin Majalisa dai ya yi aiki marar inganci a nan, don haka ya dace a yi watsi da rahoton nata. Duk jami’an da ke da hannu cikin wannan aika-aika, ya kamata a hukunta su kuma a samar da tsarin da zai hana kara afkuwar irin haka. Haka kuma, ya dace Hukumar SSS su biya diyya ga iyalan mamatan.