Gwamnatin Jihar Kano ta gwangwaje makahon nan da yake koyarwa kyauta a wata makarantar sakandare inda ta dauke shi aiki a matsayin malamin makaranta, mataki na bakwai.
Da wannan a yanzu makahon, Dahuru Abdulhamid Idris, ya zama cikakken ma’aikacin gwamnati kuma malamin makaranta mai cikakken albashi.
- ICPC na binciken shugaban KAROTA kan zargin zamba
- Idan na samu aikin gadi zan bar kasuwanci — Matashi
Wannan tagomashi ya biyo bayan rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa a ranar 25 ga Satumban da ya gabata da kuma makamancin rahoton na bidiyo.
“Hakika mun ga rahoton wannan hazikin mutum mai nakasa. Daga nan na ga ya dace mu gana da shi inda na nemi a kawo shi ta hanyar jaridar Daily Trust.
“Bayan ya zo mun je gaban Mai girma Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje, inda ya ba shi shawarwari na kwarin gwiwa. Sannan ya bayar da umarnin a dauke shi aiki a matsayin malamin makaranta.
“Ina amfani da wannan dama domin nuna godiya ga Mai girma Gwamna bisa wannan babban alheri da ya yi. Sannan ina mika godiyata ga jaridar Daily Trust bisa wannan rahoto,” inji Kwamishinan Ilimi na jihar Kano, Alhaji Muhammad Sanusi Sa’id Kiru, a zantawarsa da wakilinmu jim kadan bayan ganawarsu da Gwamnan.
Tun farko dai wani bawan Allah wanda ya nemi a sakaya sunansa ya saya wa Malam Dahuru gida na Naira miliyan biyu da dubu 400 da kuma samar musu da kayan daki domin ya zauna da iyayensa.
Hakan ya biyo bayan kwazo da jajircewa da ya gani a tare da makahon a rahoton na Daily Trust, kamar yadda mutumin ya bayyana wa wakilinmu.
“Mutane irin su Dahuru kalilan ne a duniya. Babban abin da ya ja hankalina shi ne yadda bai bari nakasa ta sa ya yi bara ba.
“Sannan da kudirinsa na son ya zama wani a rayuwa. Da kuma yadda ya zabi ya yi aikin koyarwa kyauta saboda Allah.
“Wannan abu ne mai kyau,” inji mutumin wanda ya nemi a sakaya sunansa.
Shi dai Malam Dahuru an haife shi da larurar makanta, kuma ya taso a haka har ya yi karatu tun daga firamare zuwa Kwalejin Ilimi inda ya samu takardar Shaidar Malanta ta Kasa (NCE) bisa taimako da kwarin gwiwa da yake samu daga mahaifiyarsa.
A yanzu Dahuru yana karatunsa na digiri a fannin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Karatu Daga Gida (NOUN).
Ya samu gurbin karatun digirin ne kyauta bayan da aka yi wata hira da shi a gidan rediyo da Ingilishi.
Hakan ne ya ja hankalin Shugaban Jami’ar NOUN a wancan lokaci, Farfesa Abdallah Uba Adamu, inda ya ba shi gurbin karatu kyauta a jami’ar.
Malam Dahuru ya kasance mutum mai zuciyar neman na kansa, kuma bai bari nakasar da yake da ita ta kashe masa
zuciya ba.
Hakan ya sa bayan kammala karatunsa na NCE ya yi ta fama da neman aiki amma bai samu ba.
Daga bisani sai ya yanke shawarar koyarwa kyauta, inda ya samu wata sakandare a kusa da gidansu, duk saboda kada ya zauna a gida babu sana’a ba aiki.
Dahuru ya bayyana cewa babban burinsa a rayuwa shi ne ya samu aikin yi domin ya guje wa yin bara, wacce a cewarsa tana kawo kaskanci da mutuwar zuciya.
Ya ce yana son ya dogara da kansa domin ya tallafa wa iyayensa wadanda da ma talakawa ne da kuma taimaka wa ’yan uwansa nakasassu.
Tun bayan fitar wannan rahoto na jaridar Daily Trust, Dahuru yake ta samun canji a rayuwarsa, kama daga saya masa gida da wani bawan Allah ya yi, da aiki da ya samu bayan ganawarsa da Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da sauran abubuwan da suka biyo baya ciki har da tallafin karatu da ya samu daga wata gidauniya da ake kira da Near Foundation, inda za su ba shi Naira dubu 10 a duk wata har zuwa karshen karatunsa.
“Babban burina a bangaren karatu shi ne na zama malamin jami’a, domin kuwa ina so in yi karatu har zuwa digiri na uku.
“Ina so in nuna wa duniya cewa mu ma nakasassu za mu iya duk abin da kowane dan Adam yake yi.
“Sannan ina so in zamo misali ga ’yan uwana nakasassu domin su ma su tashi su nemi ilimi domin dogara da kansu,” inji Dahuru yayin da yake bayyana burinsa a rayuwa ga Aminiya.
Game da tagomashin da ya samu, Dahuru ya ce har yanzu ya kasa yarda cewa da gaske ne domin kuwa yana ganin abin kamar a mafarki.
“A kullum gani nake kamar zan farka in ga cewa a mafarki wadanan abubuwa suke faruwa.
“Amma ga shi tabbas a gaske ne. Ban taba zaton a cikin dan karamin lokaci zan rabauta da tarin abubuwan alheri kamar haka ba.
“Hakika ina jinjina wa jaridar Daily Trust bisa wannan namijin kokari da ta yi a kaina.
“Tun farkon da wani bawan Allah ya ba ni kyautar gida ban taba zaton samun hakan ba.
“Ashe kuma wasu abubuwan za su biyo baya. Da ma burina in samu aikin yi wanda zan rike kaina da iyayena.
“Hakika babu abin da zan ce wa dukkan wadanda suka yi min wannan sai fatar alheri da kuma fatar Allah Ya biya su da gidan Aljanna,” inji Dahuru.
A nata bangaren, mahaifiyar Dahuru ta bayyana cewa farin cikinta ba zai misaltu ba, domin kuwa tunda take ba ta taba zaton za su mallaki gida mai kyau ba a cikin wannan kankanin lokacin, amma ga shi sanadiyyar wannan rahoto har aiki ma sun samu.
A cewarta “Na sha dawainiya da Dahuru, domin kuwa ya kasance mutum mai son karatu.
“Ba ya son a ce wai ya je bara ko wani abu. Shi dai kullum karatu.
“Ganin hakan ya sa na ga babu abin da ya fi face in yi iya bakin kokarina don ganin ya cim-ma burinsa. Yanzu ga shi ya zamo mana alheri.”
Daga bisani mahaifiyar tashi ta yi godiya da addu’a ga jaridar Daily Trust bisa wannan rahoto da ya zamo silar sauya rayuwarsu.
Shi ma da yake nasa bayanin, mahaifin Dahuru, Malam Abdulhamid Idris, wanda yake fama da rashin lafiya, ya ce samun Dahuru a matsayin da kuma nakasasshe ya zame masa alheri a rayuwa, tare da kawo masa ci gaba wanda bai taba zato ba.
A karshe ya yi addu’ar fatar alheri ga dukkan wadanda suka ba da gudunmawa wajen samun wannan sauyi na alheri a rayuwarsu.
A halin yanzu dai, Malam Dahuru da iyayensa sun tare a sabon gidan da aka saya musu.
Yayin da shi kuma yake shirin fara aiki a matsayin malamin makaranta.
Sannan zai koyar ne a makarantar da ya yi firamare da sakandare, kamar yadda Kwamishinan Ilimi ya bayyana.