✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rahama Sadau za ta sako wani fim mai suna dan Iya

Shararriyar ‘yar wasan fim din Hausa Rahama Sadau, ta dauki nauyi kuma ta fito a wani sabon shiri mai suna dan Iya. Za a sako…

Shararriyar ‘yar wasan fim din Hausa Rahama Sadau, ta dauki nauyi kuma ta fito a wani sabon shiri mai suna dan Iya.

Za a sako fim din ne watan Maris na shekarar 2018, sannan kuma Yunusa Mu’azu da Abba Sadau ne suka shirya, sannan Yaseen Auwal ya bada umarni.

Shirin dan Iya, shiri ne na bandariya da kamfanin Rahama Sadau na Sadau Pictures ya dauki.

A cikin fim din akwai shahararrun ‘yan wasa irinsu Rahama Sadau, Sadik Sani Sadik wanda ya fito a matsayin dan Iya, Rabi’u Rikadawa, and Aminu Sheriff Momoh da dai sauransu.

Idan ba manta ba, an dakatar da Rahama Sadau daga yin fim ko kuma fitowa a fim din Hausa a ranar 3 ga watan Oktobar badi, bayan kungiyar MOPPAN, reshen Jihar Kano ta zarge ta da fitowa a wani waka da bai dace ta fito ba mai taken ‘I lobe U’ da mawakin nan dan Jos mai suna Classik.

Tun daga nan ake ta dambarwa. Da farko ta nuna cewa bat a da masaniya a kan dakatar da ita da aka yi, sai kuma daga baya ta fito da nemi afuwar kungiyar, a wata katarda da aika wa kungiyar. Sannan daga baya kungiyar t ace ta samu takardar, sannan kuma za ta duba.

Tun wannan lokacin ake ta zaman sauraron jin tab akin kungiyar. Sai kuma kwatsam ta fito a wannan sabon shiri mai suna dan Iya wanda ta dauki nauyi.

Ita dai Rahama Sadau tana da dumbin masoya a fadin Arewacin Najeriya, da kuma yankin Kudancin kasar. Kuma tana da dumbin mabiya a shafukan zumunta na yanar gizo.

kungiyar MOPPAN dai ba tace komai ba a kan wannan sabon shirin na Rahama Sadau har yanzu.