✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rabuwar kai kawai APC ta tsinana – Sule Lamido

Ranka ya dade mu fara da nasarar da Jam’iyyar PDP ta samu a Kotun Koli, inda Sanata Ahmed Makarfi ya zama sahihin shugaban jam’iyyar ta…

Ranka ya dade mu fara da nasarar da Jam’iyyar PDP ta samu a Kotun Koli, inda Sanata Ahmed Makarfi ya zama sahihin shugaban jam’iyyar ta kasa. A matsayinka na jigo a PDP, wannan na tabbatar da cewa kun dinke barakar da ta shafe kusan shekara biyu a tsakaninku?

Wato abin da nake so ka gane tukuna shi ne, ita Jam’iyyar PDP an kafa ta ce a kan tsari. Kuma a yanzu ta shekara 20 wanda idan aka dauke su cikin shekarunka kana yaro karami! Amma a yanzu kun kai munzalin da za ku yi maganar siyasa. Manufar ita ce, ba za ka kafa jam’iyyar siyasa ba a yau, sai ka san mene ne tarihin kasarka a jiya. Da farko mene ne Najeriya tukun? Yaushe ta samu ’yancinta? Sannan a kan wace manufa? Muna maganar shekara fiye da 50 baya. Sannan mene ne mafarkin iyayenmu na wancan lokaci? Su Ahmadu Bello da Malam Aminu Kano da Tafawa Balewa da Nnamdi Azikiwe da Awolowo da irin su Akintola da Okpara da Tarka da sauransu?  To idan ka fahimci manufar wannan gwagwarmaya har aka samu ’yanci, me zai sa ka kawo maganar addini ko kabilanci a cikin siyasa? Sannan su Turawan Ingila da suka mulke mu a lokacin nan Gwamna ake turowa kuma ba Musulmi ba ne, sannan da aka zo bayar da mulkin kai sai aka ce a damka kasarku a hannunku ku ’yan Najeriya dukanku a matsayin ’ya’ya ba bayi ba. Ba kasar Musulmi ba ce, ba ta Kirista ba! Ba ta Hausawa ba ce ba ta Ibo ko Yarbawa ba, a’a tarayya ce ta ’ya’yan Adam. Wadda ta kunshi ’yanci daga mulkin Turawa a zo a mulke su da dukiyarsu  ta hanyar hadin kai da gina kasa kamar kowacce a duniya. Wannan shi ne manufar samun mulkin kan Najeriya. Saboda haka shekara 20 da suka gabata, Adamu Ciroma da Abubakar Rimi da Solomon Lar da Bola Ige da Sunday Awoniyi da Aled Ekweme da Sanata Ila da Jerry Gana da ni kaina mu tara muka batun kafa PDP. A lokacin mun ga marigayi Abacha yana so ya mike ya yi mulkin farar hula ba tare da tube kakin soja ba, muka ce ba mu yarda ba! Saboda wannan aka yi ta rigima da mu. Sai muka zauna muka ce daga samun mulkin Najeriya zuwa mutuwar Abacha abubuwa da yawa sun faru, an yi juyin mulkin 1966 wanda ka kashe Firimiya da Tafawa Balewa da sauran manyan Arewa. Sannan an zo an yi Yakin Basasa shekara uku, dan Najeriya yana kashe dan uwansa dan Najeriya! Shekara bakwai fa kacal da karbar mulki aka yi wannan. Sai kuma aka zo aka yi juyin mulkin Murtala, aka zo aka kashe Murtala, sannan Obasanjo ya karba bayan shekara biyu aka mai da mulkin hannun farar hula. Shagari ya zama Shugaban Kasa aka yi shekara hudu Buhari ya zo ya yi juyin mulki. Daga nan aka koma mulkin Babangida, aka koma mulkin Shonekan, Abacha ya juya shi bayan wata uku! To inda nake son in kai ku shi ne, wajen kafa PDP a lokacin mun kalli tarihin Najeriya a matsayin kasa, bayan mun kalli abubuwan da suka faru na masifu, sai muka ce to duk jam’iyyar siyasar da za a kafa, a kafa ta a kan mutuncin dan Adam tukun, dan Najeriya wanda yake da ne a kasarsa! Mai iko mai ’yancin zama komai a kasarsa na mukamin zabe daga kansila har zuwa Shugaban Kasa. Da wannan manufar muka kira kowa da kowa muka kafa wannan jam’iyya, kuma an sa basira da hikima da hangen nesa a cikinta.

Saboda haka zuwa yanzu duk wanda yake so ya yi siyasa a PDP to ga yadda zai yi. Daga shi Makarfi har shi Sheriff din, ba su san mece ce PDP ba a 1998! Saboda ba sa cikinta, amma yanzu ka zo ka ce ana rigima tsakanin wani bangare da wani. Domin tafiya ake yi ana gina ta, har ta kawo shekara 16 tana mulki. Jam’iyyar da ta yi Shugaban Kasa guda uku, ta yi gwamnoni fiye da 50, ta yi shugabannin Majalisar Dattawa har shida, ta yi shugabannin Majalisar Wakilai shida, ta yi ministoci sama da 100, ta yi ambasadoji sama da 100. Haka idan ka je jihohi tsakanin kwamishinoni da ’yan majalisar jiha da shugabannin kananan hukumomi da kansiloli ga su nan birjik.

Don haka akwai akwai tarihi a bayanta, ta fi karfin a ce wai ta kasance bangare-bangare. Sai dai kawai ka ce an shiga annoba a wannan yanayi! Rigima ake a cikin jam’iyya, amma maganar ita ce wanda ya shigo ta bako, wajen zumudinsa bai fahimci mene ne tarbiyyar siyasa ba. Modu Sheriff shekararsa nawa a PDP? Bai wuce biyu ba, shi dan APP ne, a nan ya yi Sanata ya yi Gwamna, amma hakika yana da ’yancin ya shigo jam’iyyar, amma kamata ya yi ya fahimci mece ce tarbiyyar PDP? Mene ne al’adunta da dabi’unta da matakan sarrafa ta? Ka ga duka bai sani ba. To wannan abu shi ya kawo har wadansu ke cewa bangare-bangare. Amma yanzu me ya faru? An yanke hukunci ko? To kafin ma yanke hukuncin, idan ka kula da dukan tarukanmu na Fatakwal da sauransu ai Makarfi ne shugaba, don haka Makarfi wakilin PDP ne, ba wakilin kansa ba ne. Sannan shi ma Sheriff ai kawo shi aka yi a matsayin wakilin PDP, sai aka ga bai dace ba aka sake shi, to mene ne abin rigima a ciki? Kuma ina gaya maka tuni gwamnoninmu da tsofaffin da ’yan majalisunmu muka yi matsaya cewa Makarfi ne wakilinmu, amma Sheriff ya ce bai yarda ba. Amma alhamdulillahi an gama, yanzu ba ma Sheriff ba, hatta wanda yake APC abin da ke gabansa kawai shi ne wane hali Najeriya take a yanzu? Me ya kamata ay i? Don haka abin da yake na ainihi ya kamata a zo a gyara a tsamo Najeriya daga halin da ta shiga.

Akidar PDP da kake magana, yawancin jama’a musamman matasa da ’yan taratsin siyasa ba su sani ba. A yanzu wadanne turaku kuke burin kafawa ta yadda nan gaba wadansu ba za su yi shigar burtu su farraka ku ba?

Wato shi dan Adam duk yadda za ka yi da shi, yana da nasa kura-kuran da kuma ra’ayinsa na mulki ko na siyasa da sauransu, domin tsarin mutum ne ba na Allah ba. Don haka dole a samu kura-kurai. Na biyu, ita siyasa farko a gina ta a kan ’yanci, yadda ake fassara haka shi ne kamar a cikin aji da malami da daliban duk ajinsu daya, tunda kowa shi ya kawo kansa. To haka kasar take, yadda malami yake da ’yanci haka dalibi yake, yadda babba yake da ’yanci haka yaro, ’yancin jahili shi ne ’yancin mai ilimi, ’yancin talaka shi ne ’yancin basarake. Don haka ’yanci ne ke hada siyasa, amma dole wurin shigar kowa da irin fahimtarsa. Wani buri, wani kokarin gina kasa, wani hadama da sauransu. Dole siyasa ta hada ire-iren wadannan mutanen. Misali abu mafi a’ala shi ne shugabanci, to amma idan shugaba ya fadi magana sabanin mabiyi, shi ke nan sai ya ki yarda! Tunda farko an hadu a kan ’yanci ne. Ka ga ke nan da malamin da dalibin ikonsu daya, to yaya za ka yi? Illa kawai duk yadda za ka yi a siyasa lallai a sanya adalci, a sanya da’a da biyayya a wajen gina ta, idan akwai adalci za a samu biyayya, idan ka samu biyayya za a samu da’a, idan aka samu da’a za a samu zaman lafiya. Saboda haka babu maganin da za ka ce ba za a samu matsala ba, domin kowa mutum ne, shi kuma mutum tara yake ba goma ba. Amma dai adalci yana taka rawa kwarai a sha’anin tafiyar da dan Adam.

Ana samun kiraye-kiraye daga sassan kasar na a sake fasalin tsarin kasar baki daya. Me za ka ce kan haka?

Tamabayar tukun ita ce me ya samu kasar? Kila idan an tambaye ka ba ka da amsa. Amma ni zan gaya maka cewa mu ne muka kafa jam’iyya muka tallata ta, muka ci zabe muka kafa gwamnati tsawon shekara 16 muna mulki, aka zo aka ce ba mu iya ba, mun gaza, mun zama annoba, mun zama jaraba, mu ne masifa, mu ne talauci, mu ne sata, mu ne Boko Haram. Duk wani dau’i na masifa da jafa’i an gaya mana a mulkinmu! To yanzu mun sauka, dan Najeriyar da ya yi hukunci a baya ai sai ya yi hukunci a yanzu, domin dukanmu ’yan Najeriya ne. Idan a hukunce-hukunce aka yi wancan hukunci cewa mu ne annoba da sauransu har aka kau da mu, ke nan ashe an yi zabin da ake ganin zai kawo alheri ne. Ka ga ashe ka tambaye ni me ake ciki, ba ta taso ba! Yanzu tambayarka za ta koma ne ga wanda ya yi zaben, idan su da kansu sun ce eh lallai a yanzu abubuwa ba su tafiya yadda ya kamata sabanin baya, to sai in ba da amsa. Idan sun amince abin da suka fada a kan PDP sharri ne kawai don a bata mu, to ashe an gano cewa muna yi musu adalci da sanin hakkin mutane, masu tausayi, idan an yarda a haka sai in ba da amsa. Amma kila ka samu amsa a nan gaba idan an zo zabe, domin an ga mulkin PDP kuma an ga na APC. Idan kasa ta yi dadi a ci gaba da APC, idan kuma an yarda ana cikin wahala to sai a koma inda aka fito. Domin sun san jiya sun san yau, shafuka biyu ne kawai, na PDP da aka kafa don hada kan ’yan Najeriya, wadda shekara 20 haka muke a PDP. Nan shafin kuma na APC, jam’iyyar gidan haya, dan AD ya koma ACN yanzu ya samu haya a gidan APC, da dan APP ya koma ANPP ya zo haya gidan APC da kuma dan CPC. Amma mu PDP muna nan a gidanmu na asali ba mu sake ba. Idan mulkin ’yan haya shi ya fi, to shi ke nan sai a yi APC, idan kuma gidan asali shi ya fi, sai a dawo a yi PDP, ai shekara hudu baya babu APC ko? To sai a gwada a gani.

Kana da ra’ayin APC ta gaza a mulkinta ke nan?

Ai gazawar APC a sarari take kowa yana gani. Kamar yadda na gaya maka cewa gidan haya ne, yadda dan ACN ya zo ya shiga haka dan PDP ya shiga, ka ga dukansu babu mai cewa gidansa ne balle a yi maganar gado. Idan ka kula irin wannan tsari na gamin- gambiza ba zai wadatar da Najeriya ba, ai ka ga yadda suke fada a tsakaninsu, babu jituwa sam! Idan ka nazarci kasar nan wacce ke da kabilu da addinai da al’adu daban-daban ai ta fi karfin wadansu su hadu daga jam’iyyu a dare daya su ce za su kai ta ga gaci. Dole sai mulkin da yake ya san mece ce matsalar kasar, sannan ‘ya’yanta su hadu daga kowane bangare su yarda da hakan su kawo ci gaban da ya kamata, amma ba APC ba. Saboda haka kamar yadda Buharin yake cewa jiki magayi, to idan jikin ya ji sai a koma inda aka fito.

Me za ka ce kan yunkurin neman raba kasa da Ibo ke yi, rashin adalci ne ko tawaye ne kawai?

To kalli yanayin ka gani! Kalli Arewa a da bisa yanayin siyasarta da jam’iyyunta, amma a yau ina jin jihohi biyu kadai suka rage a Arewa, duk APC ta mamaye ko’ina, amma cikin shekara biyu kacal, sannan ka kalli shekara hudu baya kafin zuwan APC ka ga yaya kasar take! Kai za ka yi hukunci, a wancan lokacin ana maganar Biyafara? A wancan lokacin ana cewa dan Kudu ya bar Arewa? Duk wani abu da ke kawo barazana ga kasar nan a lokacinmu babu shi. Saboda haka idan mulkin da ake yi a kasa babu adalci, to ba yadda za a yi a samu zaman lafiya. Domin kowa da ne a Najeriya. Yadda Buhari yake da, kai ma haka kake da a kasar nan ko daga ina ka fito. To idan haka ne, babu wanda zai zo ya yi mulkin son zuciya a ce za a samu zaman lafiya. Don haka duk abin da kake ganin yana faruwa a yanzu, masu mulkin ne ba su iya ba, sannan ba su da kwarewar da za su rike Najeriya a dunkule! Domin shekara biyu ke nan amma kowa so yake ya wargaje.

Amma wadansu na dora alhakin boren Ibo bisa rashin zabar APC a 2015, me za ka ce?

Wato idan aka kafa siyasa aka sa ’yan takara, kana da ’yancin ka ce ba ka son wane ba za ka zabe shi ba. Yin haka ba laifi ba ne! Babu inda aka ce dole ka zabi wane a tsarin siyasa. Idan ka sa ’yancinka ka zabi wane aka yi zabe bai ci ba, shi ke nan magana ta kare, sai wanda ba ka son ya ci, to cin nan da ya yi a karkashin jam’iyyarsa zai kai shi ga karbar kasar, a karkashin karbar nan kuma akwai rantsuwa, kuma an tsara rantsuwar cikin sigar cewa “Ni wane, a matsayina na shugaban Najeriya, zan yi adalci ga dukan ’yan Najeriya, a yayin mulkin ba zan kawo kowane irin bambanci ba.” Wannan fa shi ne rantsuwar. Ka ga babu kuma maganar jam’iyya, dukan hakkin ’yan Najeriya yana wuyanka da wanda ya zabe ka da wanda bai zabe ka ba. Kowa yana da ’yanci a matsayinsa na dan kasa, yanzu ba mu miliyan 200 ne a Najeriya ba? To amma an ce masu zabe miliyan 70, ke nan akwai kimanin miliyan 130 a waje, sannan idan ka dubi sakamakon zaben 2015 duk kuri’un mutum miliyan 30 ne da wani abu cikin miliyan 200, sannan ta Buharin miliyan 16 ce kacal, to ina sauran? Shi ke nan sai ka zo za ka gallaza wa wani saboda bai zabe ka ba?  Da tsoho da yaro da mace da namiji da Musulmi da arne da Kirista duk suna da hakki a cikin gwamnati, tasu ce ko sun yi ka ko ba su yi ka ba. Don haka adalci ke tsayar da mulki ba zalunci ba. Amma ka ce sai wanda ya zabe ka za ka yi wa aiki ai ban san yadda zan kwatanta haka ba gaskiya. Misali ni Sule Lamido ko na zabi Buhari ko ban zabe shi ba, dole ya yi mini aiki a matsayina na dan kasa, ya tsare dukiyata da lafiyata da sauran bukatu, amma mulki ko ina so ko ba na so dole ya mulke ni, wannan ba makawa, saboda shi ne Shugaban Kasa. Lallai ba mu zabe shi ba, amma tunda aka fitar da sakamako aka ce shi ya ci zabe, dole mun hakura babu yadda za mu yi. Amma maganar aiki babu bambanci.

Akwai kiraye-kirayen cewa Sule Lamido ya fito takarar Shugaban Kasa a 2019, shin za ka yi takarar?

Kullum abin da nake cewa, kasa irin Najeriya mai tarihi mai kwarjini da yawan mutane, a irin wannan yanayi har Allah Ya daga wani cikin mutum miliyan 200 a hango shi, to wannan mutum ko wane ne ya kamata ya yi wa Allah godiya. To alhamdulillahi cikin wadannan mutane al’umma a hango Sule Lamido cewa ya dace ya tsaya takara, to abin godiya ne kwarai. Sannan wa na kai, wa na fi? Wannan abu dai na Allah ne kawai. Sannan in gode wa ’yan Najeriya da suka ga dacewar in tsaya. Amma ban da wannan, idan jam’iyyata ta PDP ta ga dacewa ta a kan in yi mata takara, to zan amsa. Haka kuma ina kara godiya ga ’yan Najeriya da suke mini wadannan kiraye-kirayen.

Yallabai, ka yi Gwamna shekara takwas a Jihar Jigawa, kuma ana lissafa ta cikin jihohin da suka samu ribar dimokuradiyya. Wane tanadi ka yi musamman ga kasa mai yawan al’umma da al’adu mabambanta?

Wato abin da yake ba ni tsoro da kuma mamaki shi ne, mu ’yan Najeriya mun dauke wa kanmu cewa muna da wani hakki ga dukiyar kasarmu. Ka nemi mukami a wajen bayin Allah a siyasance, su ba ka amanar kansu ka shugabance su ce ka sarrafa mana dukiyarmu, sannan a zo a ce wai an yi aiki ana mamaki. Wannan shi ne yake ba ni mamaki wallahi. Domin idan ba ka yi aikin ba me za ka yi? Wato hadarin, a nan kasar nan mun dauke kauna babu wani hakki a kan dukiyar da aka ba mai mulki. Ni ban ga wani kokari ba idan aka ba ka amana ka kiyaye, da ma abin da ka zabe ka, ka yi ke nan. A lokacin da nake Gwamna a Jigawa, na sha fada wa ma’aikata cewa su sani suna da matakai biyu a aikinsu, na farko su ma’aikata ne za su yi aiki a biya su, na biyu kuma su ’yan Jigawa ne. Misali idan kana aiki a Ma’aikatar Ruwa ne, to idan ka yi aikinka da gaskiya, kila akwai mahaifinka a kauye zai sha ruwan, haka ma’aikacin lafiya da ilimi da sauransu, idan ka yi haka sai a ce ka yi kokari? Don haka idan ka ba ni amanar Najeriya zan tsare musu cikin duk abin da suke da hakki cikinsa. Idan ka lakanci siyasa kuma ka kware a kanta, to cikin kankane lokaci za ka warware matsalolin kasar nan, ba wata wuya!

A jiharka ta Jigawa, akwai kiki-kaka kan zaben kananan hukumomin da aka yi kwanaki. Mene ne matsayin PDP?

To ai wannan abu ne mai sauki, shugabanci a kullum yana tare ne da bin doka da oda. Misali dauki shari’ar Musulunci, ayoyin Makka ai na kira ne, su kuma galibin na Madina a kan sha’anin dokoki ne, yi kaza bar kaza domin a samu zaman lafiya. Idan aka ce a kasa babu doka, to mun koma dabbobi. Saboda haka zaben da aka yi a Jigawa saba doka ne, domin kotu ta hana, amma Gwamna Badaru ya ce sai ya yi, kuma ya yi. Kuma abin sha’awa nan ita ce, idan yana da wata bukata ga wata dokar yana bin ta, idan ba ta yi masa ba sai ya ki bin ta. Misali ni ya kai ni kotu cewa ina son in kawo hayaniya a Jihar Jigawa, sannan aka kai ni gidan yari duk da cewa Gwamna na yi a jihar nan, sannan akalla ko ban haife shi ba, ni babban wansa ne. Sannan mukamin da na rike a baya shi ne yake yi a yanzu. To amma ya kai ni kotu aka kulle ni na bi doka, amma shi yanzu a kai hukumar zabe kotu, kuma ta ce a tsaida zabe shi ya ce ba zai bi ba, to yanzu a nan gaba ya sake kai wani kotu har a yanke masa hukunci? Saboda haka ita doka idan an yi ta, kamata ya yi a bi ta. Don haka zaben da aka yi na kananan hukumomi a Jigaya duk mai hankali ya san abu ne da aka yi bisa ganganci, kuma danne hakki ne. Kuma na fada cewa duk wanda ya karbi albashi a wannan kujera sai ya biya! Domin sai an sake sabon zabe in dai akwai doka a Najeriya.  

A karshe mene ne sakonka ga dukan ’ya’yan PDP?

Sakona gare su shi ne shugabannin PDP a Najeriya su sani cewa kowa yana da hakki a kasar nan. Domin ita ce ta san hakkin shugabancin da rike kasar nan, ta rike majalisunta, ta rike jihohinta. Bayan mun yi wannan mulki ya fita a hannunmu mun ga irin koma bayan da aka samu bisa dan kuskure kadan kawai da muka yi, to yanzu sai mu tashi tsaye don sake kare wa Najeriya hakkinta kamar da. Domin idan ba PDP, babu mai iya rike Najeriya, saboda ga shi an gwada an gani babu inda ka je.