✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Qafar hagu

Addu’ar tsohuwa Wata tsohuwace ta kasa tsallake titi sai ga wani soja ya zo zai tsallakar da ita. Suna cikin tafiya sai tsohuwa ta ce:…

Addu’ar tsohuwa

Wata tsohuwace ta kasa tsallake titi sai ga wani soja ya zo zai tsallakar da ita. Suna cikin tafiya sai tsohuwa ta ce: “Allah sa ka gama da duniya lafiya.” Ya ce: “Amin Baba.” Ta ce: “Allah sa ka rabu da iyayenka lafiya.” Ya ce: “Amin.” Ta sake cewa: “Allah Ya ba ka abin da kake nema duniya da lahira.” Ya ce: “Amin Baba.” Ta sake cewa: “Allah Ya kara maka girma a kan aikinka.” Ya sake cewa: “Amin Baba.” Sai tsohuwa ta ce: “Allah Ya sa a tura ku Maiduguri ku yaki ’yan Boko Haram. Sai sojan nan ya yi sauri ya ce wa tsohuwa: “Ba amin ba!”
Daga Muhammad Kuraye, 07037583877

Batun haihuwa

Wani yaro ne ran nan sai uwarsa ta haihu, yaro ya yi ta murnar cewa ya samu kanwa. To, dama babansa yana da katon tumbi; ranar suna ana shagali sai ya shigo. Shi kuwa yaro ya tarbe shi da gudu, ya shafa tumbin ya ce: “Baba kai kuma yaushe za ka haihu, mu sha suna kamar na mama?”
Daga Abubakr A. G. Fagwalawa Kano, 08060233375

Santin kunu

Wani Babarbare ne ya je bakunta gidan Fulani, aka kawo masa kunun shinkafa da gyada mai kyau. Da ya sha sai ya ce: “Kai, ashe shanunku sun iya yin nono mai dadi.”
Daga Abubakar Gambo gadawo Kumo, Jihar Gombe, 08065672785

kafar hagu

Wasu yara ne suka je wasan kwallo da yara irinsu, ana cikin buga kwallo sai aka ci masu masaukin baki, sai suka ce ba ci ba ne. Ana cikin rigima to akwai wani mahaukaci a gefe yana kallo, sai suka tambaye shi cewa: “Malam don Allah, wannan ci ne ko kuwa?” Sai ya ce: “A’a ba ci ba ne.” Suka sake tambayarsa ya fada masu dalilin da ya ce ba ci ba ne, sai ya ce: “Saboda ai da kafar hagu ya buga kwallon.”
Daga Junaidu Iliya dangulbi, 08032342258