Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin, ya amince da shirin aiki da mayakan sa-kai, ciki har da na kasashen waje don ci gaba da yakar Ukraine.
Putin ya shaida wa Ministan Tsaron Kasarsa, Sergie Shoigu, cewa idan suka ga mai sha’awar taimaka wa ’yan awaren gabashin Ukraine a yakin da ke gudana, su taimaka musu wajen karasawa fagen daga.
- Yadda APC ta sake shiga ‘rudanin’ shugabanci
- ’Yan siyasa sun koka da kamun ludayin sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea
A cewar Shoigu, fiye da mayakan sa-kai 16,000 ne, akasarinsu daga Gabas ta Tsakiya ne suka mika bukatar shiga yakin da Rasha ke yi da Ukrine.
A kan batun makaman da aka samar daga Yammacin Turai, wadanda akasarinsu suka shiga hannun sojojin Rasha kuwa, Shugaba Putin ya ce, za a mika su ga bangaren sojin ’yan awaren gabashin Ukraine.
Putin ya kuma umarci Tinistan tsaron da ya shirya wani rahoto na musamman a kan yadda za a karfafa tsaron iyakokin Rasha da Yammacin Turai, duba da matakin da kungiyar tsaro ta NATO ke yunkurin dauka daga bangaren.