✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PSG da Barcelona da Madrid suna rububi kan Mohammed Salah

Rahotannin da suka fito daga Ingila a shekaranjiya Laraba sun nuna kulob-kulob da dama sun fara rububi a kan dan kwallon gaba na kulob din…


Rahotannin da suka fito daga Ingila a shekaranjiya Laraba sun nuna kulob-kulob da dama sun fara rububi a kan dan kwallon gaba na kulob din Liberpool Mohammed Salah.

Mohammed Salah dan asalin Afirka kuma haifaffen Masar, kawo yanzu ya zura kwallaye 37 a duk wasannin da ya yi wa kulob din Liberpool a kakar wasa ta bana.

Rahoton ya ce  manyan kungiyoyi ciki har da Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa da FC Barcelona da kuma Real Madrid da ke Sifen ne suke rige-rige a kokarin dauke dan kwallon a karshen kakar wasa ta bana.

Rahoton ya kara da cewa tuni kulob din Liberpool ya aza farashin Fam miliyan 200 kwatankwacin Naira biliyan 102 ga duk mai bukatarsa.

Idan aka sayi dan kwallon a kan wannan zunzurutun kudi, to zai kafa sabon tarihi a matsayin dan kwallon da babu mai tsadarsa a tarihin kwallon kafa a fadin duniya. 

A watan Janairun da ya gabata ne kulob din Liberpool ya sayar wa Barcelona da dan kwallonta Phillipe Coutinho a kan Fam miliyan 145 kwatankwacin Naira biliyan 74.

A bara ne Liberpool ta sayo Mohammed Salah daga kulob din Roma na Italiya a kan Fam miliyan 34 kwatankwacin Naira biliyan 17 sai ga shi yanzu tana kokarin sayar da shi fiye da Naira biliyan 100 wanda hakan ya nuna ba karamar riba za ta samu a kansa ba.