✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Pogba ya kafa sabon tarihi

dan kwallon Jubentus da ke Italiya Paul Pogba ya kafa sabon tarihi bayan ya canza sheka daga kulob din zuwa na Manchester United da ke…

dan kwallon Jubentus da ke Italiya Paul Pogba ya kafa sabon tarihi bayan ya canza sheka daga kulob din zuwa na Manchester United da ke Ingila a kan Fam miliyan 89 kwatankwacin Naira biliyan 44 da Miliyan 945.
Yanzu dai Pogba, dan shekara 23 ya kasance shi ne dan kwallon da ya fi tsada a duniya.  Ya doke tarihin da dan kwallon Madrid Gareth Bale ya kafa a shekarar 2003 bayan ya canza sheka daga kulob din Tottenham na Ingila zuwa na Madrid a kan Fam miliyan 85 kwatankwacin Naira biliyan 42 da miliyan 925.
Rahoton ya nuna Pogba ya sanya hannu ne a kwantaragin shekara biyar da yiwuwar tsawaita kwantaragin zuwa shekara 6 idan ya nuna kwazo.