✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Perez ya jinjina wa Zidane

Shugaban kulob din Real Madrid na Sifen Florentino Perez ya jinjina wa kocin rikon kwarya na kulob din Zinedine Zidane saboda sabon tarihin da ya…

  Zinedine Zidane riqe da kofin zakarun kulob na TuraiShugaban kulob din Real Madrid na Sifen Florentino Perez ya jinjina wa kocin rikon kwarya na kulob din Zinedine Zidane saboda sabon tarihin da ya kafa a kulob din na lashe kofin zakarun kulob-kulob na Turai (UEFA Champions League) a karo na 11.
Shugaban ya ce tarihin da kocin ya kafa sun hada da ya taba lashe wannan kofi a shekarar 2002 a lokacin da yake buga wa kulob din kwallo sannan ya lashe a masayinsa na Matimakin Carlos Ancelotti a shekarar 2014 ga shi kuma ya lashe a matsayinsa na koci a shekarar 2016.
“Ya shiga kundin tarihi a kulob din Madrid kuma don haka ne muka jinjina masa”, inji shugaban.
Idan za a tuna, kimanin watanni shida kenan da Zinedine Zidane ya zama kocin Real Madrid bayan kulob din ya kori Rafa Benitez saboda rashin tabuka abin kirki.
Amma bayan kocin ya karbi ragamar horar da kulob din ne ya samu nasarar zama na biyu a teburin gasar La-Liga ta Sifen sannan ya zama zakara a gasar zakarun kulob-kulob na Turai a bana.
Ga dukkan alamu mahukunta Madrid za su sabunta wa Zidane kwantaragi don ya cigaba da horar da kulob din a kakar wasa mai zuwa.