Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce, yana tausaya wa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathnan dangane da yadda ya yi watsi da Jam’iyyar PDP.
Sule Lamido ya bayyana hakan ne a hirar da ya yi da gidan talabijin na ARISE wanda kuma ya dauki hankalin jama’a musamman a dandalin sada zumunta.
- Tsohon Shugaban Kasa Jonathan ya zama dan gudun hijira
- Ni da Jonathan muka fara rattaba hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a zabe – Buhari
Tsohon gwamnan ya zargi Jonathan da yin watsi da Jam’iyyar PDP da ta gina shi, ta mutunta shi, ta kuma sa aka san shi a duniya, kafin nan shi ba kowa ba ne, babu wanda ya san shi.
“Tsohon darakta ne, ya zama mataimakin gwamna, sannan ya zama gwamna, sai ya zama mataimakin shugaban kasa, ya kuma zama shugaban kasa …. duk wadannan PDP ce sanadi” in ji Sule Lamido.
Sai ya ce, amma yanzu babu sakayyar da Jonathan ya yi wa jam’iyyar illa watsi da ita, don haka yake jin bakin ciki da takaici da abin da Jonathan ya yi wa PDP.
Sannan ya ce, shi kansa babu irin bakin jinin da bai yi ba saboda Jonathan, har kiran sa fasto sai da aka yi a Arewa saboda tsohon shugabana kasar, saboda da tsangwama.