Jam’iyyar PDP ta yi Allah wadai da harin da wasu bata-gari dauke da makamai suka kai wa gangamin yakin neman zabenta a Jihar Kaduna.
Jam’iyyar a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaranta na Kasa, Debo Ologunagba, ya fitar a Abuja a ranar Litinin, ta bayyana harin a matsayin abun takaici.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Burodi Ya Hargitsa Rayuwar ’Yan Najeriya
- Na dukufa wajen magance tsadar kayan abinci —Buhari
Ologunagba ya ce, “Makasudin masu wannan aika-aika shi ne kawo cikas ga taron dan takarar shugaban kasa na PDP, ya haddasa tashin hankali da zubar da jini a Jihar Kaduna.
“Wannan ya saba wa yarjejeniyar zaman lafiya da jam’iyyun siyasa suka rattaba wa hannu a ranar 28 ga watan Satumba na ’yan takarar shugaban kasa.
“Harin da aka kai a yau (Litinin) dole ne ya jefa ’yan Najeriya masu kishin kasa cikin damuwa, yayin da wasu rahotanni ke zargin cewa wani dan takarar gwamna a Jihar Kaduna ne ya jagoranci mummunan harin da aka kai wa yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP,” a cewarsa.
Ologunagba ya ce wadanda suka kai harin sun tsorata saboda farin jinin Atiku Abubakar da kuma yadda ya samu karbuwa ga ’yan Najeriya.
“A kowane hali, jam’iyyarmu ba za ta daga hankalinta game da hare-haren irin wadannan tsagerun ba, damuwarta ita yadda ’yan Najeriya ke nuna kauna ga Atiku da kuma PDP.
“PDP na yin jinjina kan yadda al’ummar Jihar Kaduna suka fito domin su nuna kauna duk da barazanar da suka fuskanta.
“Muna jinjina wa kokarin da jama’a ke yi na ganin an samu nasarar gudanar da gangamin, muna kara jaddada goyon baya ga Atiku tare da kara jaddada cewa Jihar Kaduna gida ta PDP ce, inda Atiku ya samu kuri’u masu tarin yawa a zaben shugaban kasa na 2019.
“Ya kamata a fahimci cewa a tarihi, mutanen Kaduna ba matsorata ba ne, musamman kan kudurinsu na zaben sa a matsayin shugaban kasa nan ba da jimawa ba.”
Ologunagba ya ce jam’iyyar PDP na yi wa sabbin wadanda suka sauya sheka zuwa cikinta maraba, musamman daga Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna da ma kasa baki daya.
“Kaduna Jiha ce mai cike da tarin jama’a, duba da irin yadda aka kwararowa zuwa PDP, wannan ya nuna mutane sun karbe ta ba tare da la’akari da kabilanci ko bambamcin addini ba,” in ji shi.