A duk lokacin da aka shiga shekarar jajibirin zabe a kasar nan sai ka ga irin yadda shugaban kasa da ke kan karagar mulki da mukarrrabansa suke kidimewa, ta yadda suke dukufa cikin kai gauro su kai mari, su shiga nan su fita can, su kulla wannan, su kwance wancan da aniyar lallai ko ana ha maza, ha mata sai shugaban kasa ya kai labari, ba ma tare da la`akari da cancantarsa ba a lokacin, walau ta tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa ko na jam`iyyarsa, bare kuma `yan kasa da su za su yi zabe.
Mai karatu kila zai iya tuna irin abubuwan da gwamnatin tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasasnjo da `yan kanzaginsa irinsu tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ibrahim Mantu suka rinka yi a karkashin Kwamitin hadin gwiwa na Majalisun Dokoki na kasa na gyaran kundin tsrin mulkin kasa da ke karkashin jagorancin Sanata Mantu a shekarar 2006, da aniyar ganin lallai “TAZARCEN” Obasanjon ta tabbata, amma Allah Ya kashe ta da rana tsaka. Kar ka yi batun kokarin TAZARCEN da tsofaffin shugabannin kasa na mulkin soja Janar Ibrahim Babangida da Janar Sani Abacha, su ka yi ya yi, amma bisa ga yadda Allah ke kishin bayinSa Ya kashe“TAZARCEN” da rana tsaka.
Ba abin da kan fado mani a zuciya a duk lokacin da na ga irin wannan hauma-hauma, irin ta a mutu ko a yi rai ta shugabanni ,a cikin mulki irin na dimokuradiyya mai cike da tanade-tanaden hawa da sauka akan karagar mulki, sai irin kalaman tsohon shugaban jam`iyyar PDP na kasa baki daya Yarima bincent Ogbulafor, ta fado mani, wanda lokacin da giyar mulki ta kwashe shi yake cewa jam`iyyarsu sai ta kwashe shekaru 60, cif-cif, tana mulkin kasar nan ba kakkautawa. Sai kuma in rinka tunanin cewa shin ko bisa ga wancan hasashe na Yarima bincent, shugabannin PDP, suka rufe idanuwansu su rinka aikata dukkan abin da ya raya masu? Ba ma tare da la`akari da makomar kasar ta fannin zaman lafiyarta da ta al`ummarta ba, wanda sai da shi duk wani mai kwadayin mulki zai yi mulkin.
Abin da ya sa na ce haka, bai wuce irin yadda karara yanzu ta bayyana jam`iyyar PDP, ta sa manya-manyan abokan hamayyarta na jam`iyyar APC gaba don ganin lallai sai ta gama da su don kawai ta samu cimma burinta na sake tsayar da tabbatar da nasarar shugaban kasa Jonatahan a zaben 2015, bisa ga irin yadda ta afka wa gwamnonin babbar jam`iyyar adawa ta APC. Na san mai karatu ya ji cewa a ranar waccan Larabar 16-07-14, Majalisar Dokokin jihar Adamawa ta tsige Gwamnan Jihar Alhaji Murtala Nyako, bisa ga wai samunsa da aikata wasu laifuffuka 16, da Majalisar Dokokin jihar ta zarge shi da aikatawa, laifuffukan da kwamitin da ya binciki gwamnan ya tabbatar da aikata su.
Abin dubawa anan, shi ne dukkan laifuffukan da Majalisar Dokokin ta zayyana, kama daga yin sama da fadi da dubban miliyoyin kudin gwamnatin jihar da na Majalisun kananan Hukumominta da nada iyalinsa a mukaman gwamnati, duk laifuffuka ne da Majalisar ta yi bincike akan , ta kuma san da zaman ya aikata su, tun a shekarar 2008, amma a lokacin tunda yana cikin jam`iyyar PDP, ba laifuffuka ba ne, bare su sa ta tsige shi, sai bayan da ya kasance cikin gwamnonin PDP biyar da suka bar jam`iyyarsu ta PDP, suka koma jam`iyyar adawa ta APC a watan Nuwambar bara. Sauran gwamnonin da suka yi waccan canjin sheka tare da shi, sun hada da Dokta Rabi`u Musa Kwankwaso na jihar Kano da Mista Rotimi Amaechi na Jihar Riibas da Alhaji Aliyu Magatakarda Wammako na Sakkwato da Alhaji Ahmed Abdulfatah na Jihar Kwara. Sai Cif Rochas Okorocha na Jihar Imo da ya rungumi APC daga wani bangare na jam`iyyarsu ta APGA.
Maganar da ke kasa yanzu ita ce, wasu daga cikin wadancan gwamnoni da na ambata a sama da wasu `yan asalin jam`iyyar APC irin su Alhaji Tanko Al-Makura na jihar Nassarwa da Kwamared Adams Oshiomohle na Jihar Edo da gwamnonin jihohin Barno da Yobe Alhaji Kassim Shettima da Alhaji Ibrahim Gaidam yanzu duk suna fuskantar barazanar tsigewa daga gwamnatin tarayya ta PDP, bisa ga zargin aikata laifuffukan da idan da gwamnatin tarayya za ta waiwayi gwamnoninta 18, da ta taras da abubuwa masu muni akan tafiyar da gwamnatocin jihohinsu, kodai kwatankwacin na jihohin jam`iyyar adawar koma wadanda suka dara su.
Yanzu mai karatu dauki rigimar da ake yi a jihar Edo, `yan Majalisar Dokokin jihar hudu ne rak suka yi canjin sheka daga jam`iyyarsu ta APC, suka koma ta PDP, kuma a zaman tsarin aiki na Majalisar Dokoki, sauran takwarorinsu suka dakatar da su daga halartar zaman Majalisar na wani lokaci, amma wadannan `yan Majalisa hudu su Rundunar `yan sandar jihar take ba kariya akan lallai sai sun koma Majalisar ta kowane hali, duk da niyyar a wargaza gwamnatin jihar.
A Jihar Barno, tshohon gwamnan jihar ne Sanata Ali Modu Shariff ya yunkuro da karfin gwamnatin tarayya, suke kokarin ko-ana-ha-maza ha-mata, sai ya raba Gwamna Alhaji Kassim Shettima da kujerarsa kafin ma zaben 2015, ya nada nasa. Irin wannan yunkuri yake a makwabciyar jihar ta Yobe, alhali gwamnatin tarayya ta manta cewa rikicin `yan kungiyar Jama`atu Ahlis Sunnah LidDa`await Wal Jihad, ana zargin Sanata Modu Shariff ya assasashi tun yana kan karagar mulkin jihar tsakanin 2003 zuwa 2011.
Dukkan wadannan yunkuri PDP na yinsu ne lokacin da ake kasa da watanni bakwai da babban zaben shekarar 2015. Ana kuma zargin PDP din kan yi wa `yan Majalisun Dokokin jihohin alkawarin ba su makudan kudi, da kuma samun takara kai tsaye a zabubbukan 2015, din.
Ba wai wani sabon labari ba ne a ce an tsige gwamnan jihar tun daga jamhuriya ta biyu zuwa yau, amma abin da ke sabon labarin shi ne irin yadda jam`iyya mai mulki ta PDP, take neman ta sa gwamnonin adawa gaba akan sai ta ga bayansu. Ai gwamnatin tsohon shugaban kasa Cif Obasanjo ta tsige wasu gwamnonin jihohi hudu, wadanda duk `yan jam`iyyar ta ne tsakanin watan Disamban 2005 zuwa na Disamban 2006, su ne Dapire Alamieyeseigha na Jihar Bayelsa da Kayode Fayose na jihar Ekiti, wanda yanzu ya sake cin zaben gwamnan jihar a watan Yunin da ya gabata da Mista Joshua Dariye na jihar Filato, da Cif Ladoja na jihar Oyo.
Duk da yake jami`an jam`iyyar PDP da na gwamnatin tarayya sun ta musamta zargin suna da hannu cikin yunkurin tsige gwamnonin jam`iyyar adawar. Kome ke gaskiya ko rashin gaskiyar masu mulkin, babban abin da ya fi dacewa ga gwamnatin tarayya yanzu bai wuce ta dukufa ka-in da-na-in wajen tabbatar da cewa ta dauki dukkan matakan da suka wajaba wajen kawo karshen annobar rikice-rikicen rashin zaman lafaiya ta tashin bama-bamai da kashe-kashe da a kullum suke ta karuwa a sassa daban-daban na kasar nan. Dubi dai irin harin yunkurin daukar rayuwa da aka kaiwa tsohon shuugaban kasa, kuma jigo a cikin jam`iyyar adawa ta APC Janar Muhammadu Buhari da Sheikh dahiru Usman Bauchi shahararren Malamin addinin Islama din nan dukkansu a Kaduna akan kuma titi daya a ranar Larabar da ta gabata. Ya kamata gwamnatin PDP ta sa ni cewa masu magana kan ce, dan da ya hana uwarsa barci shi ma ba zai yi ba.
Ina yi wa dukkan al`ummar musulmin duniya Barka da Sallah, da addu`ar Allah Ya karbi ibadarmu.
PDP: dan da ya hana uwarsa barci shi ma ba zai yi ba
A duk lokacin da aka shiga shekarar jajibirin zabe a kasar nan sai ka ga irin yadda shugaban kasa da ke kan karagar mulki da…