✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ozil ya kafa sabon tarihi a Firimiya

Jaridar UK Sun ta Ingila ta ce dan kwallon Arsenal Mesut Ozil ya kafa sabon tarihi a matsayinsa na dan asalin Jamus da ke buga…

Jaridar UK Sun ta Ingila ta ce dan kwallon Arsenal Mesut Ozil ya kafa sabon tarihi a matsayinsa na dan asalin Jamus da ke buga kwallo a gasar Firimiya ta Ingila bayan ya zura kwallo a ragar kulob din Leicester City a ranar Litinin da ta wuce, inda Arsenal ta lallasa City da ci 3-1.

Rahoton ya ce yanzu Mesut Ozil ya zura kwallaye 30 a raga a gasar ta Firimiya ta Ingila kuma ya sha gaban tsohon dan kwallon Tottenham wanda shi ma ya fito daga Jamus Jurgen Klinsmann wanda ya taba zura kwallaye 29 a raga.

Ozil, wanda yake da shekara 30 ya taba buga wa kulob din Real Madrid na Sifen kwallo kafin ya canja sheka zuwa Arsenal.

Tauraruwar dan kwallon tana haskakawa a kakar wasa ta bana, inda kawo yanzu ya taimaki kulob din Arsenal wajen samun nasara a wasanni 10 a jere a duk wasannin da kulob din ya yi.

A hira da ya yi da manema labarai jim kadan bayan an tashi wasa a ranar Litinin, dan kwallon ya bayyana farin cikinsa game da wannan nasara da ya samu kuma ya yi fatan takwarorinsa da ke kulob din Arsenal za su ci gaba da nuna kwazo don ganin sun lashe kofuna a bana musamman Kofin Firimiya na Ingila.