✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Omicron na kawo tsaiko ga harkar lafiya —WHO

WHo ta ce nau'in Omicron na iya haifar da tsaiko a harkar kwion lafiya a duniya baki daya.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce Omicron na haifar da yawaitar masu kamuwa da COVID-19, wanda kuma ke kawo tsaiko ga harkar kiwon lafiya a duniya.

Ghebreyesus ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a birnin Geneva, inda ya ce yanzu lokaci ne da ya kamata kasashen duniya su mayar da hankali wajen samar da rigakafin cutar.

WHO na tsoron cewa Omicron na iya haddasa rashin yarda da rigakafin COVID-19 a tsakanin al’umma, ganin yadda kasashe masu karfi ke yi wajen samar da rigakafin.

A makon jiya ne wata kungiyar nemna tabbatar da daidaito wajen rabon rigakafin, ‘People’s Vaccine Alliance’, ta ce a cikin mako shida Amurka da kasashen Tarayyar Turai da kuma Birtaniya sun samu alluran da ta zarce yawan wanda aka samar wa nahiyar Afirka a tsawon shekarar 2021.

Kazalika, WHO ta bukaci kasashen da su mayar da hankali wajen tallafa wa kasashen Afirka da rigakafin a kan lokaci, saboda yadda cutar ke dada mamaye a nahiyar.

A makonnin baya, sai da Najeriya daga nahiyar Afrika, ta lalata allurar rigakafin COVID-19 guda miliyan daya da wa’adin aikinsu ya kare, wanda hakan ya sa hukumomin kasar suka ce ba za su sake karbar rigakafin da ya kusa daina aiki ba.

Tuni aka fara takfa muhawara a tsakanin manyan kasashen duniya kan rashin alfanun barin allurar rigakafin ba tare da raba wa kasashen da suke da bukata a kan lokaci ba.