✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obama da shugabannin Amurka sun yi wa Trump rubdugu

Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya caccaki magajinsa Donald Trump na jam’iyyar Republican da yi wa shugabancin kasar riko tamkar ‘wasan kwaikwayo na kai tsaye’.…

Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya caccaki magajinsa Donald Trump na jam’iyyar Republican da yi wa shugabancin kasar riko tamkar ‘wasan kwaikwayo na kai tsaye’.

A jawabinsa na yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar jam’iyyarsa ta Demokrat Joe Biden, Obama ya ce Trump “ya kasa girma ya iya jan ragamar mulkin kasar yadda ya kamata kuma ba zai iya ba”.

“Abin da ya dame shi shi ne amfani da ofsihinsa ya taimaki kansa da mukarrabansa.

“Ya mayar da shugabanci tamkar wasan kwaikwayo da yake amfani da shi domin jan hankalin mutane yadda yake so”, inji Obama.

Obama wanda Biden ya yi wa Mataimakin Shugaban Kasa, ya fadi hakan ne a ranar Laraba bayan tsoffin shugabannin kasar karkashin jam’iyyar, Bill Clinton da Jimmy Carter da sauransu da kuma tsohon Sakataren Tsaro Collin Powell daga jam’iyyar Republica suka yi kace-kaca Trump.

— Yadda Trump ya mayar da martani

Sai dai a martanin Trump, ya ce Amurkawa sun zabe shi ya gaji Obama ne saboda “tashin hankalin” da gwamnatin Obama ta jefa kasar.

Da yake mayar wa magabacin nasa martani, Trump ya ce, “Abin da bari a matsayin shugaban kasa shirme da tashin hankali.

“Kun ga gazawarsa a matsayin shugaban kasa; Rashin tabukawar Shugaba Obama ya sa aka zabe ni na hau kan mulki”, inji Trump

— Shugabannin Demokrat sun yi wa Trump rubdugu

A jawabansu ga magoya bayan Demokrat, Clinton da Jimmy Carter da Powell sun bayyana goyon bayansu ga Biden a matsayin mutumin da ya fi dacewa ya jagoranci Amurka ta bangaren dabi’u da kwarewa.

Clinton ya ce: “Duk da zaman kasar mafi karfin tattalin arziki a cewar Trump, amma a nan kasar kadai rashin aikin yi ya ninku sau uku.

“Maimakon Ofishin Shugaban Kasa ya zama cibiyar shugabanci, Trump ya mayar da Fadar White House cibiyar rikici.

Sun kuma caccake shi da  ‘goyon baya da taimakon masu kama-karya, amma yake raba gari da manyan kawayen Amurka’.

Tsohon Sakataren Harkokin Waje John Kerry ya ce: “Duk lokacin da wannan shugaban ya je kasar waje to sai ya yi abun kunya.

“Ya bata da kawayen mu amma yana goyon bayan azzalumai. Amurka na bukatar shugaba da za a yi koyi da shi ne ba wanda aka mayar abun dariya ba”, inji shi.

— Trump makaryaci ne, inji Colin Powell

A nashi bangaren, Collin Powell wanda aka saba gani a tarukan jam’iyyar Trump ta Republican ya ce Trump ‘makaryaci ne’ kuma ya bayyana goyon bayansa ga Biden

Powell na daga cikin ‘yan jam’iyyar Republikan da suka fito suka bayyana goyon bayansu ga Mista Biden, ciki har da gwamnan Ohio John Kasich.

— Kamala Harris ta yi kasa-kasa da Trump

Hakan na zuwa ne a yayin da ‘yar takarar Mataimakin Shugaban Kasar Demokrat Kamala Harris ta amshi takarar da jam’iyyar ta ba ta.

Ta ce gwamnatin Trump’ ta ba Amurkwa kunya kuma ta gaza sauke nauyin da ke kamata.

Kamala Harris da Joe Biden dan takarar shugaban kasan Demokrat na kalubanatar Shugaba Trump da mataimakinsa Mike Pence masu neman wa’adi na biyu a zaben ranar 3 ga watan Nuwamba.