✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obafemi Martins ya zura kwallonsa ta 17 a Amurka

Shahararren dan kwallon Najeriya Super Eagoles da yanzu haka yake kwallo a kulob din Seattle Sounders a gasar rukuni-rukuni na Amurka ya zura kwallonsa ta…

Shahararren dan kwallon Najeriya Super Eagoles da yanzu haka yake kwallo a kulob din Seattle Sounders a gasar rukuni-rukuni na Amurka ya zura kwallonsa ta 17 a kakar wasa ta bana a ranar Lahadin da ta gabata, bayan kulob dinsu ya lallasa na Colorado Rapids da ci 4-1.
Obafemi Martins ne ya zura kwallaye biyu daga cikin kwallaye hudun.
A halin yanzu kulob din Sounders na daya daga cikin kulob biyu da ke sahun gaba tare da na Los Angeles Galady a gasar, bayan sun hada maki 60 kowannensu.
Sai dai Martins ba ya cikin ’yan kwallon da kocin Najeriya Stephen Keshi ya gayyato wadanda za su kece raini da kasar Sudan a gasar neman hayewa gasar cin kofin Afirka da zai gudana a gobe Asabar a filin wasa na Sudan ba.