Kungiyar Malamai ta Najeriya (NUT) ta yi kira ga gwamnonin jihohin da malaman makaranta ke bi bashi da su yi amfani da dan lokacin da ya rage musu a kan karagar mulkin su biyan hakkokin.
Sakatare-Janar na kungiyar, Dokta Mike Ike-En ne ya yi wannan kira ranar Talata a Abuja albarkacin zagayowar Ranar Malamai ta Duniya wadda za a yi ranar Laraba.
- Zakarun Turai: Yadda za a fafata a wasannin Daren farko
- An kori manyan ’yan sanda 7, an rage wa 10 matsayi kan rashin da’a
A cewar Ike-Ene, akwai gwamnoni da dama da ba su kammala biyan bashin albashin da malaman firamare da na sakandare ke bi a jihohinsu ba.
Don haka ya ce akwai bukatar gwamnonin da lamarin ya shafa su yi kokarin biyan malaman hakkokinsu a tsakanin ‘yan watannin da suka rage musu a kan mulki.
“Yawancin malaman sun koka kan rashin biyan su albashi a kan kari duk da tsadar rayuwar da ake fama da ita.
“A wasu jihohin, malaman firamare na bin gwamnatin jihar bashin albashi na watanni hudu zuwa 18,” in ji Ike-Ene.
Ranar 5 ga watan Oktoba ta kowace shekara Majalisar Dinkin Duniya ta ware don gudanar da bikin Ranar Malamai ta Duniya da zummar yabawa da kuma karfafa wa malaman makaranta gwiwa a fadin duniya.