✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nura M. Inuwa ya karyata batun cewa ya samu karuwa

Fitaccen mawakin fina-finan Hausa, Nura M Inuwa ya karyata labarin da ake yadawa cewa ya samu karuwa. Mawakin ya bayyana hakan ne a lokacin da…

Fitaccen mawakin fina-finan Hausa, Nura M Inuwa ya karyata labarin da ake yadawa cewa ya samu karuwa.

Mawakin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya tattauna da wakilin Aminiya.

A lokacin da ake yada labarin an sanya hoto mai dauke da mutum uku, inda a hoton mawaki Nura M Inuwa da kuma jarumi Adam A Zango suka sanya wani matashi a tsakiya wanda yake rike da jariri a cikin farin tawul.

Mawakin ya ce rahoton da ake yadawa ba gaskiya ba ne, domin hoton da aka yi amfani da shi wajen yada labarin sun je ne don taya wani masoyin Adam A Zango murna sakomakon karuwa da aka yi masa.

Ya ce, “Wannan rahoton ba gaskiya ba ne, kamar yadda aka gani na samu qaruwa, maganar gaskiy ita ce, murna muka je yi wa wani bawan Allah wanda masoyi ne ga Adam A Zango, kuma shi ma ana kiransa da A Zango, shi ne ya samu karuwa, wannan ita ce maganar gaskiya a takaice.”

Mawaqin ya bukaci mutane su guji yada jita-jita domin hakan ba dabi’a mai kyau ba ce.