✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NUJ a Gombe ta horar da ‘yan jarida 97 cikin shekara daya – Kwamred Malala

Shugaban Kungiyar  ‘Yan Jarida ta kasa reshen Jihar Gombe, Kwamred Sa’idu Bappah Malala ya ce cikin shekara daya, kungiyar ta sami nasarar horar da mambobinta…

Shugaban Kungiyar  ‘Yan Jarida ta kasa reshen Jihar Gombe, Kwamred Sa’idu Bappah Malala ya ce cikin shekara daya, kungiyar ta sami nasarar horar da mambobinta guda 97 ta fuskar sanin makamar aiki, gabanin babban zaben da ya gudana cikin shekarar nan.

Horon dai, ya hada da yi wa ‘yan jaridar bitar yadda za su ba da rahotannin zabukan.

Shugaban, ya ce mambobinsu da dama sun samu halartan tarurrukan karawa una sani a ciki da wajen jihar ta Gombe. Kuma kungiyar na kokarin samar wa dukkanin ‘ya’yan kungiyar da katin shaidar aikin jarida a jihar.

Ya ci gaba da cewa yanzu haka suna nan kungiyar NUJ ta dukufa ka’in da na’in wajen ganin ta kammala aikin ginin katafaren Sakatariyarta na jiha, inda ya nunar da cewa, an kusan cimma aikin a yanzu haka da kashi 80 cikin 100.

Kwamred Malala, ya kuma ce duk da kasancewar kungiyar ba ta kammala ginin Sakatariyar ba, a yanzu ta sami tsugunar da ofishin nata na wucin gadi a ma’aikatar watsa labarai ta jihar, kafin ta kare aikin ginin.

Shugaban ya kara da cewa, kungiyar ‘yan jaridar na hirin yin hadaka da kungiyoyi masu zaman kansu dan shirya tarurrukan wayar da kan jama’a,  da zummar horar da mambobinta akan al’amuran yau da kullum, wadanda ke shafar aikin jarida a zamanin nan.

Da yake bayanin ci gaban kungiyar, ya ce tuni aka kafa kwamiti karkashin jagorancin Mataimakinsa, Musa Jibrin Tabra, kuma nan ba da jimawa ba, kwamitin zai bada rahotonsa, wanda kungiyar za ta duba shawarwarin tare da aiwatar da su don habaka aikace-aikacen kungiyar.

Kwamred Malala, ya kuma ce baya ga wannan, kungiyar na saran tabbatar da ta hada kan mambobin kungiyar musamman sababbi da suke sa ran rantsarwa a sabbin kafofin watsa labarai masu zaman kansu a jihar ta Gombe.

A cewarsa, muddin aka yi hakan zai taimaka wajen karfafa gwuiwar masu aikin jarida a duk inda suke a jihar Gombe. Kuma NUJn na saran inganta kula da hakkoki da kuma kare mutuncin ‘yan Jaridar a ko’ina a fadin jihar.

A game da Ishorar kiwon lafiya kuwa, Kwamred Malala, ya nunar da cewa, suna sauraron uwar kungiyar ta kasa, inda nan ba da jimawa ba za ta kaddamar da shirin tare da kara inganta shi ta yadda zai shafi dukkan mambobinta, ba ma sai mambanta ya rasa ransa ba, a’a za a samar da Inshora na kula da lafiyan mamban kungiyar. Inda ya kawo misali cewa a jihar akwai mambobinta guda biyu dake da bukatar kulawa ta musamman-wadanda suka hada da Muhammad Ibrahim Pantami da Abubakar Sadik Ahmad, da suke fama da jinya tsawon lokaci.

Ya ce kungiyar na aiki ba dare ba rana wajen ganin an samar da wani tallafi a kungiyan ce da zai taimakawa wadannan ‘yayan kungiyar da ma sauran ire-irensu da ke fama da wasu matsaloli na rashin lafiya.

Da yake tsokaci akan haikewa ‘yan jarida da jami’an tsaro suke yi a wasu lokuta, ya ce NUJn ta shirya tsaf dan kalubalantar wannan al’amari, sakamakon abinda ya kira ‘aikin jarida ba ta’addanci bane’ kuma ya ce ba za su lamunci cin zarafin ‘yan jaridarsu ba.

A karshe ya yi kira ga ‘yan jaridar da su gudanar da ayyukansu bisa ga tsarin kundin mulkin kungiyar da kuma dokoki da aka tanada na aikin don ciyar da sana’ar gaba.