✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NSCDC ta ba iyalan jami’inta da aka kashe a harin Kuje N2.8m

Hukumar ta kuma yi alkawarin daukar ’yar marigayin aiki

Rundunar tsaro ta NSCDC ta bayar da kudi Naira miliyan biyu da dubu 800 ga iyalan marigayi Insfekta Iliyasu Abraham, jami’inta da aka kashe lokacin da ’yan bindiga suka kai hari gidan yarin Kuje.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar kuma Mataimakin Babban Kwamnada Olusola Odumosu ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Odumosu ya ce Babban Kwamnandan Rundunar, Ahmed Audi, ya ba da cekin Naira miliyan biyu da rabi, da kuma kudi a hannu Naira dubu 300 ga matar marigayin da diyarsa.

Baya ga kudin, sanarwar ta ce Babban Kwamandan ya yi alkawarin daukar diyar marigayin Abimiku Abraham aiki a  sabbin ma’aikatan da za su dauka a nan gaba.

Ya kuma mika ta’aziyarsa ga iyalin, tare da tabbatar musu da cewa za a ci gaba da tunawa da marigayin a matsayin jarumin da ya rasa ransa ya na kokarin kare kasar sa.

Haka kuma, Kwamanda Audi ya yi kira ga hafsoshi da shugabannin shiyyoyin rundunar da na jihohi da su hada hannu da sauran rundunonin tsaro wajen samar da sabbin dabarun tunkarar kalubalen tsaron Najeriya.

Ya kuma shawarci sauran al’ummar Najeriya da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanai masu amfani kuma a kan lokaci domin dakile ayyukan ta’addanci.