✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NRC ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a fadin kasa

Sai bayan zabe za su ci gaba da aiki

Hukumar Sufurin Jirgin Kasa ta Kasa (NRC) ta ba da sanarwar dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a fadin kasa daga ranar Asabar, 25 zuwa Litinin, 27 ga Fabrairu.

Hukumar ta ba da sanarwar hakan neranar Talata, ta bakin kakinta, Mahmood Yakubu, a Legas.

Ya ce an dauki wannan mataki ne domin bai wa ’yan kasa damar kada kuri’a a zabe mai zuwa.

A cewarsa, jiragen da lamarin ya shafa su ne, na Abuja-Kaduna da Warri-Itakpe da Legas-Ibadan da kuma Lagos-Ijoko.

Jami’in ya ce jiragen za su ci gaba da aiki a ranar Talata, 28 ga Fabrairu.

(NAN)