Hukumar Sufurin Jirgin Kasa ta Kasa (NRC) ta ba da sanarwar dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a fadin kasa daga ranar Asabar, 25 zuwa Litinin, 27 ga Fabrairu.
Hukumar ta ba da sanarwar hakan neranar Talata, ta bakin kakinta, Mahmood Yakubu, a Legas.
- Shari’ar Sauyin kudi: Kotun Koli ta je hutu
- Canjin kudi ya gurgunta ayyukan ’yan ta’adda –Rundunar Soji
Ya ce an dauki wannan mataki ne domin bai wa ’yan kasa damar kada kuri’a a zabe mai zuwa.
A cewarsa, jiragen da lamarin ya shafa su ne, na Abuja-Kaduna da Warri-Itakpe da Legas-Ibadan da kuma Lagos-Ijoko.
Jami’in ya ce jiragen za su ci gaba da aiki a ranar Talata, 28 ga Fabrairu.
(NAN)