Cibiyar binciken aikin gona ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta yi bikin baje kolin ingantaccen irin auduga domin bunkasa nomanta a kasar.
An gudanar da bikin ne lokacin taron nazarin noman auduga na shekarar 2021 da aka gudanar a cibiyar da ke Zariya.
Shugaban shirin noman audugar, Farfesa Isa Onu a jawabinsa ya ce, makasudin taron shi ne domin bunkasa iri da noman audugar domin ta karbu a kasuwar duniya.
Ya bayyana cewa, taron ya samu halarcin duk masu ruwa da tsaki a harkar noman auduga domin tantance ingancin irin da ya kamata manoma su yi amfani da shi.
Ya ce, tabbatar da ingancin irin zai sa ya samu karbuwa a kasuwanni.
Ya kara da cewa, za a kai irin jihohin da ake noman auduga inda za a bambance ingancinsa ta yadda za a bambance farashinsa.
Farfesa Onu ya bayyana cewa, ana inganta audugar ce ta hanyar shuka iri mai kyau da kuma tsaftace daurin audugar.
Da yake jawabi tun da farko, babban Daraktan Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Muhammad Faguji Ishaku ya jaddada cewa, cibiyar ta shirya taron ne domin samar da irin auduga bai daya ta yadda za ta karbu a kasuwar duniya.
Farfesa Faguji Ishaku, wanda mataimakin Darakta a Cibiyar, Farfesa Ado Yusuf ya wakilce shi ya ce, taron zai kuma yi nazarin ingancin irin da noman da kasuwancinta da matsaloli da kuma samar da mafita. Amma ya bayyana cewa masana’antar auduga ta samu tallafi daga gwamnatocin baya, amma har yanzu ba a samu canjin da zai sa Najeriya ta shiga cikin kasashen duniya da ke noman auduga ba.
Shi ma a nasa jawabin, babban sakataren kungiyar manoman auduga ta kasa, Alhaji Hassan Buhari ya ba da shawarar cewa a samar da tsarin zai samar da cibiyoyin sayar da auduga a jihohi da kananan hukumomi.
Ya ce samar da cibiyoyin zai bunkasa tattalin arziki kuma ya bunkasa samar da ingantaccen irin auduga da ya tabarbare sakamakon rashin tsarin kasuwancin audugar.
Hassan ya ce, a shekarun baya ana tantance ingancin audugar ce zuwa rukunin A,B,C wanda hakan ne zai sa amfanin da manomi ya samu ya yi daraja, domin a cewarsa ba za a amshi duk wata auduga da aka gurbata ta ba.