✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Noma ne hanyar tsira ga Nijeriya – Farfesa Dadari

Farfesa Salihu Adamu Dadari, malami ne a Sashin Binciken Aikin Gona na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. A wannan tattaunawa da ya yi da…

Farfesa Salihu Adamu Dadari, malami ne a Sashin Binciken Aikin Gona na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana cewa rungumar harkokin noma ita ce babbar hanyar tsira ga Najeriya. Ya bayyana matakan da suka kamata Gwamnatin Najeriya ta dauka don farfado da harkokin noma a kasar nan. Haka kuma ya yi bayani kan irin illolin da magungunan kashe tsirrai da kwari da manoman kasar nan suke amfani da su. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Yaya ka ga yadda harkokin noma suke tafiya yanzu a Najeriya?
Shi dai aikin noma wanda ake yi wa kirari da na duke tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar, shi ne aka fara sani a Najeriya kafin a samo man fetur.
To, amma gwamnatocin Najeriya da suka gabata ba su tallafa wa harkokin noman ba. Sai ka ga an bai wa manoma mutum 20 buhun taki daya, a ce su je su raba. Wane irin abinci ne manoma mutum 20 za su iya nomawa da buhun taki daya?
Sai a dauki babbar mota tebur daya ko biyu na takin zamani a bai wa wani dan barandar siyasa mutum daya, ya je ya sayar wa ’yan kasuwa, a sake dawowa a sayar wa da manoma. To, amma a yau wannan sabuwar gwamnati ta yi ikirarin cewa za ta kawo canji kan wannan hali da manoma suke ciki.
To, me za ka ce kan matakan da wannan sabuwar gwamnati ta dauka na farfado da aikin noma a Najeriya?
Farko, Allah Ya taimaki Shugaban kasa Muhammad Buhari ya samu Ministan Noma wanda shi kansa ya yarda da noman kuma yana noman. Kuma yana ba da shawarwari wadanda za su taimaka wa ’yan Najeriya kan harkokin noma.
Bayan haka, a cikin matakan da wannan gwamnati ta dauka na farfado da aikin noma a kasar nan, akwai maganar farfado da noman auduga a Najeriya; ta yadda za a samu a farfado da masakunmu, don mutane su samu aikin yi. Domin a takaice noman auduga da masakun kasar nan, idan aka farfado da su, akalla za su iya samar wa ’yan Najeriya mutum miliyan 50 aikin yi.
Har’ila yau, wannan gwamnati ta ce za ta inganta noman shinkafa a kasar nan, domin bai kamata a rika kawo shinkafa daga kasashen waje ba. Domin shinkafar da ake kawowa daga kasashen waje, shinkafa ce wadda ta shekara 10 a ajiye, an sanya mata sanadarori na kashe kwari. Ka ga abin da ya kashe kwaro, idan ba a yi hankali ba, zai iya kashe dan Adam. Kuma shinkafar da ta shekara 10 a ajiye ba ta da wani amfani amma sai a kawo wa dan Najeriya ya kama ci. Saboda jahilcin al’amari, sai ka ji matanmu suna cewa suna son shinkafa ’yar Thailand ko shinkafa ’yar China. Amma shinkafar da muke nomawa a nan Najeriya tana da matukar amfani wajen inganta lafiyarmu. Domin shinkafarmu ba ta da wani nakasu, domin ba a sanya mata wani magani na kashe kwari ba, kuma tana dauke da abubuwan gina jiki.
Har’ila, yau wannan gwamnati ta ce za ta farfado da aikin noman rama a Najeriya, domin a dawo da buhunan garara. Saboda buhunan leda da muke amfani da su wajen sanya kayayyakin gona suna kawo ciwon kansa. Don haka wannan gwamnati ta ce za ta farfado da noman rama kuma noman rama ya fi kowanne noma sauki a duniya. Domin da ka shuka ta sai ta daga sama domin ciyawa ba ta yi mata illa.
A yanzu an fara wannan noma na rama a Najeriya, akwai wanda ya shuka eka biyar a Kano, a Zariya ma akwai wani mutum  ya shuka wannan rama eka biyar. Mu kuma a Jami’ar Ahmadu Bello, muna nan muna bincike kan wannan noma na rama. Kuma wannan gwamnati ta ce idan aka noma amfanin gona, ya yi yawa za ta saya ta ajiye a sito-sito dinta. Babu shakka idan aka cika wadannan alkawura, Najeriya za ta yi rawar gani kan aikin gona.
A matsayinka na masani kan harkokin noma, me za ka ce kan yadda manoma suke amfani da magunguna masu guba a kayayyakin amfanin gonar da suke nomawa a kasar nan?
A gaskiya wannan al’amari na amfani da magungunan kashe tsirrai da kwari da manoma suke yi a kayayyakin amfanin gonar da suke nomawa a Najeriya, wata babbar matsala ce. Domin irin wadannan magunguna suna kawo mana cututtuka da dama a kasar nan, sakamakon irin wadannan magunguna da ake amfani da su a amfanin gonar da muke nomawa a kasar nan. Za ka ga mutum yana tafiya sai kafarsa ko hanunsa ya shanye ko ka ga ciwon suga ko ciwon hawan jini ya yi sama, ko ka ga idon mutum ya rufe. Amma saboda ba mu bin doka da oda za ka ga irin wadannan magunguna masu cutarwa da manomanmu suke amfani da su a cikin kasuwanninmu da shagunanmu. Idan ka je kasuwa za ka ga mai sayar da magungunan kashe tsirrai da kwari ga kuma mai sayar tsire ko waina ’yar yau a kusa da shi. Allah Ya taimaka yanzu a kimiyyance ana nan kokarin ganin an canza wadannan magungunan kashe tsirrai da kwari masu guba, zuwa magungunan kashe tsirrai da kwari wadanda ake hada su da halittun itatuwa. Domin su wadannan magunguna ba su da illa ga mutane.
Kamar ni din nan, ina bincike kan sanadarin magungunan kashe  tsirrai na auduga da masara da dawa da gero da barkono da dai sauransu. A wannan bincike da muke yi, muna amfani da itatuwa irin su bini da zugu da dogon yaro da dai sauransu.
To, a nan wane kira ko jan hankali za ka yi ga gwamnati da manoma dangane da irin wadannan magunguna masu guba?
Ai akwai hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) amma ba su aikinsu yadda ya kamata. Saboda haka gwamnati ta dada tashi tsaye wajen ganin wannan hukuma tana aikinta yadda ya kamata, domin a ceto rayukan al’ummar kasar nan.
A karshe mene ne sakonka ga manoma da gwamnatocin kasar nan dangane da aikin noma?
Sakona ga al’ummar Najeriya shi ne mu rungumi harkokin noma kuma gwamnatocin Najeriya su tallafa wa harkokin noma. Domin noman nan shi ne hanyar tsira ga Najeriya. Manyan kasashen duniya irin su Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus da China da Kanada, dukkansu ba su yi wani tasiri ba, sai da suka rungumi aikin noma. Saboda haka idan gwamnati ta rungumi noma a kasar nan za mu kai labari.