✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NMC Ta Shirya Gasar Lissafi ga Dalibai Mata A Najeriya

A karin farko a Najeriya, Cibiyar Ilimin Lissafi ta Kasa (NMC) ta shirya gasar lissafi ga dalibai mata da ke azuzuwan karamar Sakandare. Daraktan cibiyarm…

A karin farko a Najeriya, Cibiyar Ilimin Lissafi ta Kasa (NMC) ta shirya gasar lissafi ga dalibai mata da ke azuzuwan karamar Sakandare.

Daraktan cibiyarm Farfesa Promise Mebine, ne ya bayyana hakan ranar Juma’a a Abuja, inda ya ce an shirya gasar ne domin karfafa wa daliban guiwar nazarin lissafin.

Ya ce a matakin farko, cibiyar za ta zabo dalibai 120 mafiya kwazo daga dukkanin mazabun Najeriya.

“Daga ciki mu sake zabo 20 mafiya kwazo daga kowace Jiha, wadanda da su za a je zagaye na biyu na gasar.

“Sai kuma zagaye na uku wanda za a fitar da wadanda suka fi maki guda uku daga Jihohi daban-daban, mu hada su wuri guda domin zabo wanda ya fi kowa,” in ji shi.

Daraktan ya kuma roki kungiyoyin gida da na kasashen waje, da su hada hannu da cibiyar domin daukar nauyin zakaran gasar.

Ya ce hakan zai sanya gasar koyon ilimi a tsakanin dalibai mata ’yan Najeriya wadanda aka saba barin su a baya a harkar ilimin boko.