✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nijeriya ta fitar da yazawa na Naira biliyan 146 cikin wata 6 — NBS

Har yanzu Nijeriya na kan gaba wajen sarrafa yazawa domin ana sarrafa kasa da kashi 10 a nan Nijeriya.

Nijeriya ta fitar da yazawa da ya kai na Naira biliyan 146.1 a wata 6 na farkon shekarar nan, a cewar wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar.

Rahoton mai taken Kasuwancin Kasashen Waje a Kididdigar Kayayyaki ya nuna cewa, an kasa nau’in yazawa zuwa gida biyu. Akwai yazawa da kuma kwallansa da ake fitarwa zuwa kasashen waje.

Rahoton ya bayyana cewa, a wata 6 na farko na 2023, an fitar da yazawa na adadin kudi Naira biliyan 27.1 zuwa kasashen ketare, inda Jamhuriyar Vietnam ke kan gaba wajen siya, yayin da aka fitar kwallayensa har na Naira biliyan 6.8.

A kuma wasu watanni 3 na shekarar, rahoton ya bayyana cewar, an samu karuwar fitar da kayayyakin da kudinsu ya karu zuwa Naira biliyan112.1 tare da samun karin yawaitar fitar da kwallon yazawar da kudinsa ya kai Naira biliyan 57.4, inda shi kuma yazawar aka fitar da na Naira biliyan 54.6.

Rahoton ya kara da cewa, yazawa na sama da Naira biliyan 102.3 aka kai zuwa kasar Vietnam.

Aminiya ta ruwaito cewa, adadin yawan kayan da aka fitar a farkon rabin 2023 ya zarce na Naira biliyan 116, idan aka kwatanta da yawan kayan da aka fitar a 2022 da ta gabata.

Idan dai ba a manta ba, tsohon Sakataren Hukumar Bunkasa Fitar da Kayayyaki ta Nijeriya (NEPC), Dokta Ezra Yakusak, ya bayyana a watan Afrilun da ya gabata cewa, Nijeriya ta fitar da adadin yazawa har na Naira biliyan116 (Dala miliyan 252), wanda wannan adadi ya fi na kayayyakin da aka fitar a 2022, inda hakan ya sa Nijeriya ta kasance kasa ta 4 a nahiyar Afrika da ke samar da yazawa.

Dokta Yakusak ya bayyana cewa, an fitar da ton dubu 315,677 na yazawa a lokacin da ya dace kuma ana sa ran samun karin kudin shigar da zai kai Naira biliyan 232 (Dala miliyan 504) nan da karshen 2023.

Ya bayyana cewa, adadin da aka samu a bara ya kasance na biyar a cikin kayayyakin da Nijeriya take fitarwa sabanin man fetur.

Shugaban Hukumar NEPC ya ce, “Kasuwancin yazawa a Nijeriya na samun koma baya ne saboda rashin bin ka’idojin kiyaye abinci da rashin noman sa da rashin sanin muhimmancisa da kuma yadda ake fama da tsofaffin bishiyoyin yazawa.

Haka kuma yawancin yazawan da aka sarrafa ba su da yawa, domin yana daya daga cikin kayan da mafi yawan wadanda ake fitarwa galibi na amfanin yau da kullum ne.

Sai dai Babban Sakatare na Kungiyar Masu Noman yazawa ta kasa (NCAN), Mista Sotonye Anga ya ce, kusan kaso 90 cikin 100 na yazawan da ake nomawa a Nijeriya da kuma fitar da shi zuwa kasashen waje na zama asara, saboda rashin tsarin adana shi yadda ya kamata.

“Lokacin da muke fitar da yazawa, muna kuma fitar da irin zuwa kasashen waje, don haka dole ne gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su samar da yanayi mai kyau don inganta fannin da kuma yadda za a adana shi,” in ji shi.

Ya ce, har yanzu Nijeriya na kan gaba wajen sarrafa yazawa domin ana sarrafa kasa da kashi 10 a nan Nijeriya.

Ya kara da cewa, dole ne gwamnati ta mai da hankali wajen bunkasa noman yazawa zuwa akalla kashi 30 ko 50 cikin 100.

“Dole ne a auna manufofin ta yadda za a samar da yanayi mai kyau. Dole ne mu karfafa bangaren noman yazawa a Nijeriya’’.

Ya kara da cewa, ya kamata gwamnati ta samar da gidauniyar ci-gaban noman yazawa ta kuma kara adadin kason da za ta saka a gidauniyar daga Naira biliyan 30 zuwa Naira biliyan 200 a cikin shekaru biyar, wanda hakan zai ba wa bangaren damar kasancewa daya daga cikin manyan masu bayar da gudunmawar bunkasa ci-gaban tattalin arziki a Nijeriya,” inji Anga.

Ya ce, zuba jarin zai samar da daya daga cikin hanyoyin samun kudin shiga da kuma kawo babban abin alfahari ga kasar nan.

“Komai na yazawa kamar mansa da irinsa da kwallonsa da sauransu duk ana fitar da su zuwa kasashen waje,” inji shi.